Gobarar daji na ci gaba da yadu wa a sassan jihar California ta Amurka

Gobarar daji da ta kama a ranar Litinin a Kudancin jihar Californiya ta Amurka na ci gaba da yadu wa ba sassauta wa sakamakon yadda iska ke kada wa a yankin.

A yanzu wutar ta shiga yankin Bel Air na Los Angeles.

Gidaje 200 ne suka kone a Los Angeles inda aka kuma kwashe mutane kusan dubu 200 daga matsugunansu.

An kuma bayar da daukar hotunan bidiyo na talabijin da ake yi a yankin saboda gobarar.

Labarai masu alaka