Kasashen Musulmi zaso gudanar da taron gaggawa a Istanbul akan Qudus

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya kira taron gaggawa na ƙasashen Musulmi da za'a gudanar a Istanbul a ranar 13 ga watan Disamba akan yunkurin shugaban ƙasar Amurka Donald Trump na maida birnin Qudus babban birnin lsra'ila.

Hakan dai ya biyo bayan sanarwar da fadar gwamnatin Amurka tayi da cewar shugaba Trump ya dauki damarar maida birnin Qudus babban birnin Isra'ila, a yayinda ya bada umurnin maida ofishin jakadancin Amurka dake Isra'ila zuwa birnin.

 Manyan jamiyyun huɗu na Majalisar Dokokin Turkiyya sun ƙalubalanci yunƙurin Trump na maida birnin Qudus amatsayin babban birnin lsra'ila da babban murya. 

Dayawan masu fada aji da masana sunyi nazarin cewar hakan ba zai kawo karshen rikicin Falasdinu da Isra'ila ba sai dai ma ya kara gurbata lamurkan.Labarai masu alaka