Turkiyya ta gargadi 'yan kasarta game da zuwa Amurka

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta gargadi 'Yan kasarta game da ziyartar Amurka a 'yan kwanakin nan.

Turkiyya ta gargadi 'yan kasarta game da zuwa Amurka

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta gargadi 'yan kasarta game da ziyartar Amurka a 'yan kwanakin nan. 

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta ce, tana gargadin 'yan kasarta kan ziyartar Amurka sakamakon aiyukan ta'addanci da rigingimu da ake fama da su a kasar.

Sanarwar da Ma'aikatar ta fitar ta ce, matukar dai ba ya zama wajibi ba to lallai Turkawa su guji ziyartar Amurka, sanna wadanda suke kasar su nisanci zuwa wuraren da ke da taron jama'a kamar makarantu, tashohin jiragen kasa da manyan shaguna.Labarai masu alaka