• Bidiyo

An sake kai hari da makami mai linzami zuwa Saudiyya

Saudiyya ta samu nasarar lalata wani makami mai linzami da aka harba mata daga kasar Yaman.

An sake kai hari da makami mai linzami zuwa Saudiyya

Saudiyya ta samu nasarar lalata wani makami mai linzami da aka harba mata daga kasar Yaman.

An harba makamin daga gar,in Nejran da ke kan iyakar Yaman da Saudiyya wanda aka yi amfani da garkuwar makamai masu linzami wajen lalata shi a sama.

Rundunar Kawancen Kasashen Larabawa da Saudiyya ke wa jagpranci ba ta ce komai ba game da lamarin.

Amma 'yan tawayen Houthi sun ce, su ne suka kai harin zuwa Saudiyya daga garin Nejran.

Tun bayan kifar da gwamnatin Ali Abdulah Salih Yaman ta fada yakin basasam inda a watan maris din 2015 Saudiyya ta jagoranci Kasashen Larabawa wajen kai wa 'yan tawayen Houthi hare-hare ta sama.Labarai masu alaka