Girgizar kasa ta afku a Myammar

Girgizar kasa mai karfin awo 6 ta afku a tsakiyar kasar Myammar.

Girgizar kasa ta afku a Myammar

Girgizar kasa mai karfin awo 6 ta afku a tsakiyar kasar Myammar.

Cibiyar Bincike Kan Yanayin Kasa ta Amurka ta ce, girgizar ta afku a yankin da ke da nisan kusan kilomita 120 a arewa maso-yammacin Bago.

Bayan girgizar ta farko wata mai karfin awo 4.2 da 5.3 sun sake afkuwa. 

Girgizar ta afku a karkasin kasa sosai kuma ba ta janyo asarar rai ko dukiya ba.Labarai masu alaka