Sojojin Isra'ila sun kashe yara kanana 2 a Falasdin

Sojojin Isra'ila sun kashe yara kanana 2 tare da jikkata wasu mutane 3 a yankunan Zirin Gaza da Yammacin gabar Kogin Jordan da Yahudawa suka mamaye.

Sojojin Isra'ila sun kashe yara kanana 2 a Falasdin

Sojojin Isra'ila sun kashe yara kanana 2 tare da jikkata wasu mutane 3 a yankunan Zirin Gaza da Yammacin gabar Kogin Jordan da Yahudawa suka mamaye.

Kakakin Ma'aikatar Lafiya ta Falasdina da ke Gaza Ashraf Al-Kudra ya bayyana cewa, a yayin zanga-zangar adawa da matakin da Amurka ta dauka na ayyana Kudus a matsayin Helkwatar Isra'ila a kusa da sansanin 'yan gudun hijira na Al-Barij wani yaro mai shekaru 16 Abdulhamid Abu Musaid ya rasa ransa sakamakon harbin sa da sojojin Isra'ila syka yi.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta kuma cewa, a garin Nablus na Yammacin gabar Kogin Jordan sojojin na Isra'ila sun sake kashe wani yaro Bafalasdine. 

An kashe yaron mai suna Ali Amr Kaynu mai shekaru 16 shi ma, kuma dan uwansa Nasr Kaynu ya ce, sojojin sun harbe marigayin a kofar shiga kauyen Irak Burin.

Ya ce, Ali ya mutu bayan an kai shi asibitin Nablus.Labarai masu alaka