Yadda sakamakon gwajin kwakwalwar Trump ya kasance

Asibitin Sojoji na Walter Reed da ke Amurka ya fitar da sanarwar cewa, shugaban kasar Donald Trump na da cikakkiyar lafiyar kwakwalwa da sauran sassan jiki.

An samu cece kuce ne bayan da Michael Wolff ya rubuta wani littafi game da cewa, Trump ba shi da cikakkiyar lafiyar kwakwalwa wanda hakan ya sanya bayyanar shugaban a asibiti don auna shi.

Fadar White House ta rawaito babban likitan Asibirin Dr. Jackson na cewa, bayan gwajin da suka yi sun gano shugaba Trump na da cikakkiyar lafiyar kwakwalwa da sauran sassan jiki, kuma a mako mai zuwa za a bayar da cikakken rahoton binciken. 

Ba a bayyana ainihin a wane bangare aka yi wa Trump gwaje-gwajen ba amma kuma ana hasashen an binciki kwakwalwarsa da wasu sassan jikinsa.Labarai masu alaka