Gwamnatin Indiya ta janye tallafin da ake ba wa Mahajjatan kasar

Gwamnatin Indiya ta dauki matakin janye tallafin da ta ke ba wa Musulmai a lokacin da za su je Aikin Hajji Kasa Mai Tsarki.

Gwamnatin Indiya ta janye tallafin da ake ba wa Mahajjatan kasar

Gwamnatin Indiya ta dauki matakin janye tallafin da ta ke ba wa Musulmai a lokacin da za su je Aikin Hajji Kasa Mai Tsarki.

Ministan Kula da Harkokin Jama'a 'Yan Tsiraru Muktar Abbas Nakvi ya ce, tun shekarar 1959 zuwa yau gwamnatin Indiya ke bayar da tallafi ga Musulmai a lokacin da za su Aikin Hajji amma a yanzu an janye wannan tallafi.

Nakvi ya kara da cewa, wannan taimako da ake bayarwa ba ya amfanar jama'ar Indiya nda za a dinga kashe kudaden wajen ilmantar da yaran jama'ar marasa rinjaye.

Ya ce, duk da janye tallafin a wannan shekarar ana sa ran akwai Maniyyatan Aikin Hajji dubu 175 a kasar kuma wanna adadi ne mai yawa a tariin Indiya.Labarai masu alaka