'Yan ta'addar Houthi 'Yan Shi'a na Yaman sun sake kai wa Saudiyya hari da makami mai linzami

'Yan ta'addar Houthi 'yan Shi'a da ke kasar Yaman sun sake harba makami mai linzami daga garin Jazan zuwa Saudiyya inda sojojin kasar suka yi amfani da garkuwar makamai masu linzami wajen lalata makamin.

Rahotanni sun ce ba a samu asarar rai ko jikkata ba sakamakon harba makamin.

A baya ma 'yan ta'addar Houthi sun kai hare-haren makamai masu linzami zuwa garuruwan Saudiyya daban-daban inda ake lalata makaman.

A shekarar 2014 ne 'yan ta'addar na Houthi suka yi wa gwamnati juyin mulki inda ya zuwa yau suke rike da San'a babban birnin kasar.

A watan Maris din 2015 kuma Kawancen Kasashen Larabawa Karkashin Jagorancin Saudiyya suka fara kai hare-hare ta sama don yakar 'yan ta'addar na Houthi.Labarai masu alaka