“Na je coci don zama Kirista,amma fasto ya hana ni”

Wata Musulma wacce ta nemi mafaka  a Faransa ta je coci da nufin zama Kirista, amma fasto ya gargade ta da kar ta sake Musulunci ya bukuce mata.

“Na je coci don zama Kirista,amma fasto ya hana ni”

Wata Musulma wacce ta nemi mafaka  a Faransa ta je coci da nufin zama Kirista, amma fasto ya gargade ta da kar ta sake Musulunci ya bukuce mata.

Matar ta ce : “Ni Musulma ce gaba da baya, kuma ‘yar kabilar Kabil ta kasar Aljeriya.Na fara rayuwa a Faransa tun a shekarar 2004.Na yanke shawarar zama Kirista,saboda Larabawa sun musuluntar da magabatanmu da karfi da yaji, shekaru aru-aru da suka gabata.Shi yasa na bukaci ungunlu ta koma gidanta na tsamiya,wato in sake rungumar addinin kakannina,Kiristanci.Wannan ne dalilin yasa na dukufa zuwa  coci mafi kusa tare da bayyana bukata ta ga fasto.Amma abin mamaki,sai ya sunkuyar da kai kasa, yayi dogon numfashi.Can bayan wani lokaci ya ce mun,kar na sake Musulunci ya kubuce mun,saboda Islam addini ne na zaman lafiya,kaunar juna da kuma tausayi.Wannan lamarin yayi matukar ba ni mamaki,abinda yasa kunya ta lullube ni”

 Labarai masu alaka