An kai wa jerin gwanon motocin ‘yan siyasar Turkmen harin bam a Iraki

Mutum 1 ya rasa ransa yayinda wasu 11 suka jikkata sakamakon tayar da bama-baman da aka jera a cikin wata mota da ke gefen hanya a lokacin da jerin gwanon motocin dan takarar majalisar dokokin Iraki Kahya dan kabilar Turkmen da ke garin Kirkuk ke wucewa.

An kai wa jerin gwanon motocin ‘yan siyasar Turkmen harin bam a Iraki

Mutum 1 ya rasa ransa yayinda wasu 11 suka jikkata sakamakon tayar da bama-baman da aka jera a cikin wata mota da ke gefen hanya a lokacin da jerin gwanon motocin dan takarar majalisar dokokin Iraki Ammar Kahya dan kabilar Turkmen da ke garin Kirkuk ke wucewa.

Shugaban ‘yan sandan Kirkuk Ali Kamal ya fitar da sanarwa inda ya ce, a yankin Hadra na Kirkuk, an yi amfani da na’ura daga nesa waen tayar da bama-baman da ke cikin wata a lokacin da jerin gwanon motocin dan takarar majalisar dokokin Iraki na Turkmen da ke karin Kirkuku ke wuce wa.

Kamal ya ce, babu abinda ya samu Ammar Kahya a harin amma wani farar hula 1 ya mutu, inda wasu mutane 11 da suka hada da masu tsaron lafiyarsa 2 suka jikkata.

Ya ce, har yanzu ba a gano su waje suka ajje motar a kan hanyar ba kuma wasu motoci 3 sun kone kurmus sakamakon fashewar bama-baman.Labarai masu alaka