An sake kira da a fita zanga-zanga a Zirin Gaza

Wata Kungiya Mai Kare Hakkokin Falasdinawa ta yi kira da miliyoyin mutane su fita zanga-zanga a kan iyakar Isra’ila a ranar 5 ga watan Yuni.

An sake kira da a fita zanga-zanga a Zirin Gaza

Wata Kungiya Mai Kare Hakkokin Falasdinawa ta yi kira da miliyoyin mutane su fita zanga-zanga a kan iyakar Isra’ila a ranar 5 ga watan Yuni.

Sanarwar da Kungiyar ta fitar ta ce, za a ci gaba da zanga-zangar kare Falasdinawa da ake yi a Zirin Gaza kuma a ranar 5 ga Yuni da ta yi daidai da zagoyowar ranar da aka fara mamayar yankinsu a 1967.

Kungiyar ta ce, a wannan miliyoyin mutane ne za su fita zanga-zanga a kan iyakar Isra’ila.

Haka zali Kungiyar ta nemi da a gurfanar da Shugabannin Isra’ila a gaban kotu sakamakon kisan gilla da zaluncin da suke yi wa Falasdinawa.

Kungiyar ta kuma dora alhakin rikicin da ake yi kan Amurka da Isra’ila.

A zanga-zangar da aka yi a Zirin gaza mutane 62 ne suka yi Shahada yayinda wasu dubu 2,770 suka samu raunuka.

Daga cikin wadanda suka yi Shahadar akwai yara ‘yan kasa da shekaru 18 su 8, kuma daga cikin wadanda suka jikkata akwai yara 225 da mata 86.

 Labarai masu alaka