Jaririya 'yar watanni 8 na daga cikin Falasdinawan da Isra'İla ta kashe

Falasdinawa 62 ne suka yi Shahada bayan bude musu wuta da sojojin Isra'ila suka yi a Zirin Gaza a lokacin da suka taru don nuna adawa da dauke ofishin jakadancin Amurka daga Tel Aviv zuwa Kudus da kuma cika shekaru 70 da Nakba.

Ma'aikatar lafiya ta Falasdin ta sanar da cewa, wadanda suka jikkata kuma sun kai dubu 2,770.

Sanarwar ta kuma ce, 8 daga cikin wadanda suka yi Shahada na da shekaru kasa da 18 inda daga wadanda aka jikkata kuma ake da yara 225 da mata 86. Haka zlika an jikkata mutane dubu 2770.

Daga cikin wadanda aka kashe har da jaririya Layla 'yar watanni 8 wadda ta shaki hayaki mai sa hawaye da Isra'ila ta harba.

Mahaifiyar Layla Maryam Al-Gandur ta ce, dakarun Isra'ila sun kashe mata yarinyar da ba ta gama kaunarta ba. 

Gandur ta ce, 'yarta mai fara'a da farin ciki a koyaushe ce kuma Isra'ila ce ke da alhakin kisan ta.Labarai masu alaka