Majalisar Dinkin Duniya ta yi taron gaggawa game da Falasdin

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da taron gaggawa bayan bukatar hakan da Kasar Kuwait ta nema sakamakon kashe mutane 62 da Isra'ila ta yi a Zirin Gaza.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi taron gaggawa game da Falasdin

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da taron gaggawa bayan bukatar hakan da Kasar Kuwait ta nema sakamakon kashe mutane 62 da Isra'ila ta yi a Zirin Gaza.

Wakilan kasashen duniya mambobin Kwamitin sun yi tsaiwar makokin mutane da aka kashe a wajen zanga-zangar.

A bayanin wakiliyar Amurka a Majal,isar Dİnkin DUniya Nikey Haley ta yi ta ce, suna damuwa matuka game da halin da Gabas ta tsakiya ke ciki da kuma mutuwar mutane a yayin zamga-zanga.

Ta ce, ana samu rikici sosai a yankin inda ta zargi Kwamitin da nuna halin munafurci.

Haley ta kuma dora alhakin rikicin Gaza kan Iran inda ta kare martabar Isra'ila.

Haley ta zargi Iran da tayar da zaune tsaye a Siriya, Yaman da Labanan kuma akwai bukatar a mayar da hankula kan Iran imnda za a yi batun rikici a Gabas ta Tsakiya.

Wakiliyar ta Amurka ta soki Iran da ta ke bai wa Kungiyar Hamas taimako wadda Amurka ke dauka a matsayin 'yar ta'adda.

Wakilin Bolibya a Kwamitin Sacha Sergio Llorentty Soliz ya karanta sunayen yara kanana da aka kashe a Zirin Gaza inda ya nuna bukatar da ke akwai ta Kotun kasa da Kasa da ta fara bincike kan kisan na Gaza.

Wakilin Rasha a Majalisar Dmitry Polyansky ya bukaci Netanyahu da Abbas da su sasanta juna tare da kawo karshen matsalar da ake fuskanta.

Wakilin Ingila Karen Pierce kuma cewa, ya yi Isra'ila na da hakkin kare iyakokinta amma kuma akwai bukatar sojojin Kasar su daina amfani da karfi da ya wuce kima.

Wakilin Faransa François Delattre ya yi gargadi kan yiwuwar rikicin ya yadu zuwa sauran yankunan.

Wakilin China Ma Zhaoxu,ya yi kira ga Isra'ila da ta nutsu tare da daina kashe Falasdinawa.

Wakiliyar Polan Joanna Wronecka kuma ta yi kira da a gudanar da bincike kan kisan falasdinawa 62 a Zirin Gaza.

Jami'in Musamman na Majalisar Dinkin Duniya Kan Samar da Zaman Lafiya a Gabas ta Tsakiya Nikolay Mladenov ya soki amfani da karfi da sojojin Isra'ila suka yi kan Falasdinawa.

Wakilin Falasdin Riyad Mansur kuma cewa, ya yi, shin Falasdinawa nawaake jiraba kashe kafin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya fara daukar wani mataki, yanzu da a ce a kasarku ne aka kashe mutane 60 da suka hada da yara kanana shin me za ku yi? Wannan munafurcin har zuwa yaushe zai cigaba? Labarai masu alaka