Duk dan da ya hana uwarsa barci, shi ma ba zai taba rumtsawa ba

Sakamakon binciken kwamitin leken asiri na majalisar dattawan Amurka ya nuna cewa, babu sauran tantama,Rasha ce ta kai gauro ta kai mari don ganin Trump yayi nasara a zaben shugaban kasar na shekarar 2016.

Shugaban kwamitin bincike kana wakilin Jam'iyyar Republicans na Arewacin Carolina, sanata Richar Burr ya ce:

" Babu sauran tantama,Rasha ta yi kememe yayin zaben shugaban kasar Amurka a shekarar 2016,inda ta dinka shiga da fice babu dare babu rana,har sai da ta ga Trump ya hau karagar mulki.Me zai hana mu ki yarda da wannan hujjar da jami'an leken asirin Amurka suka bankado".

Mataimakin Burr,wakilin jam'iyyar Republicans na yankin Virginia,sanata Mark Warner kuma cewa yayi,

"Rasha ta nuna hazaka da kwarewa matuka gaya.Putin ne ya bada umarni kai tsaye don a tallafa wa Donald Trump da kuma cutar da Hillary Clinton".

Shugaban kwamitin leken asirin na majalisar dattawan Amurka,Burr ya ce bayan sun kaddamar bincike-bincikensu na karshe,zasu gabatar wa duniya rahotonsu na karshe a watan Agusta mai zuwa.Labarai masu alaka