Ruhani: Amurka ta zama saniyar ware

Shugaban kasar Farisa,Hasan Ruhani ya bayyana cewa, Amuka ta zama saniyar ware a fagen siyasar duniya.

Ruhani: Amurka ta zama saniyar ware

Shugaban kasar Farisa,Hasan Ruhani ya bayyana cewa, Amuka ta zama saniyar ware a fagen siyasar duniya.

A bayanin da ya yi a wani taron aka gudanar a Tahran, babban birnin kasar,wanda kuma ya samu halartar ministocin zartawar da na shari'a, Ruhani ya yi tsokaci kan takunkuman da Amurka ta kakaba wa Iran,inda ya ce,

"A yau Amurka ta fi kasancewa saniyar ware kan batun kakabawa Iran takunkumai fiye zaminnikan baya.Gudanar da aiyukanta ta hanyar taka dokoki, yasa ko abokan ittifakinta ba su goya ma ta baya ba".

Ruhani ya kara da cewa, kawo yanzu Sin,Rasha,kasashen Turai da makwabtanta sun ki yin na'am da yunkurin na Trump.Labarai masu alaka