Saudiyya ta garkame Sheikh Safar al Hawali

Saudiyya ta garkame babban mu'addibi sheikh Safar al Hawali a kan ya soki lamirin aika-aikan 'ya 'yan masarautar, cikin wani sabon littafinsa da ya wallafa.

Saudiyya ta garkame Sheikh Safar al Hawali

Saudiyya ta garkame babban mu'addibi sheikh Safar al Hawali a kan ya soki lamirin aika-aikan 'ya 'yan masarautar, cikin wani sabon littafinsa da ya wallafa.

Daman, an taba kulle shi,saboda ya yi Allah wadai da kawayence da ke tsakanin kasarsa da sojojin Amurka.

A ranar Alhamis din nan da ta gabata, masu fafutuka sun soki Saudiyya da kakkausar murya,ganin yadda take ci gaba da tafiya wata sabuwar turba, wacce ta yi hannun riga da ta shari'ar Musulunci.

Kungiyar kare hakki bil adama ta Saudiyya, ALQST ta sanwar wa manema labaran kafar Reuters cewa, an kama malami Hawali a ranar Larabar nan da ta gabata, bayan ya wallafa wani littafi wanda a cikin sa ya soki ahlin Sa'ud.
 Labarai masu alaka