Abbas: Zamu ci gaba da kalubalantar manufofin Amurka akan Falasdin

Shugaban kasar Falasdin Mahmud Abbas ya shaidawa takwaransa na Rasha Vladimir Putin da cewa suna daukar matakan ci gaba da kalubalantar manufofin Amurka a gabas ta tsakiya da kuma Falasdinu.

Abbas: Zamu ci gaba da kalubalantar manufofin Amurka akan Falasdin

Shugaban kasar Falasdin Mahmud Abbas ya shaidawa takwaransa na Rasha Vladimir Putin da cewa suna daukar matakan ci gaba da kalubalantar manufofin Amurka a gabas ta tsakiya da kuma Falasdinu a lokacin da suke tattaunawa akan matakin Amurka na mayarda ofishin jakadancinta na Isra’ila daga Tel Aviv zuwa Qudus.

"Kanfanin dillancin labaran Rasha ta rawaito Mahmud Abbas na cewa zamu dauki dukkanin matakai wajen kalubalantar yunkurin Amurka akan Falasdin”

Abbas ya ziyarci Moscow domin ganawa da Putin kwana daya bayan Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya zirarci kasar.

Abbas ya kara shaidawa Putin cewa sun damu akan matakan da shugaba Donald Trump ke dauka akan yankin inda ya kara da cewa baya barci dare da rana domin ganin ya kalubalanci yunkurin Amurka akan Falasdin.
 Labarai masu alaka