Firaministan Yaman ya zargi Houthi da bata rayuwar jama'ar Kasar

Firaministan Yaman Ahmad bin Daar ya zargi al'umar Houthi da dagula al'amura da jefa jama'a cikin zullumi a Kasar.

Firaministan Yaman ya zargi Houthi da bata rayuwar jama'ar Kasar

Firaministan Yaman Ahmad bin Daar ya zargi al'umar Houthi da dagula al'amura da jefa jama'a cikin zullumi a Kasar.

Bin Daar ya yi jawabi bayan da 'yan Houthi sun je gidansa tare da ragargaza kayan da ke cikin a San'a Babban Birnin Yaman inda ya ce, Houthi sun hargitsa komai a Yaman hatta a albashin ma'aikata sun lalata shi, sannan kuma sun tafiyar da farin ciki da walwalar jama'a.

Ya ce, Houthi sun yada cin hanci da Rashawa a Yaman, har yanzu wasu yankunan nan hannunsu kuma suna gallazawa jama'a.

Bin Daar ya ci gaba da cewa, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da aiyuka har sai ta tabbatar da aiyukanta na ci gaba tare da samun nasara a kan 'yan Houthi.Labarai masu alaka