Shugaban Kasar Vietnem ya rasu

Shugaban Kasar Vietnem Tran Dai Quang ya mutu yana da shekaru 61 da haihuwa.

Shugaban Kasar Vietnem ya rasu

Shugaban Kasar Vietnem Tran Dai Quang ya mutu yana da shekaru 61 da haihuwa.

Gidan Rediyon gwamnatin kasar ya sanar da cewar wani mummunan ciwo ne ya yi ajalin shugaban wanda ya rasa ransa da karfe 3.05 na daren Juma'ar nan.

A ranar 2 ga watan Afrilun 2016 aka zabi Quang wanda ya samu kaso 91 cikin dari na kuri'un da aka jefa kuma tsawon shekara 1 ba a ganin sa saboda rashin lafiyar da ke damun sa.Labarai masu alaka