"Karshen Trump zai zama daya da na Saddam"

A albarkacin bikin tunawa da fafata yakin Irak da Iran karo na 38,shugaban kasar Farisa Hasan Ruhani ya ce, karshen Donald Trump zai zama daya da na Saddam Husain,saboda shi ma ya yi watsi da yarjejeniyar nukiliya.

Ruhani ya furta wadannan kalaman gabanin afkuwar harin ta'addancin Ahvaz,inda ya ce:

"Yarjejeniyar nukiliyar da muka rattaba wa hannu tare wasu kasashen Turai babban alheri ne ga Gabas ta Tsakiya da ma duniya ga baki daya.Amma ga dukkanin alamu, ana shirin maimaita hikayar Saddam Husain.Fakat,a baya Iraki ce ta saye yakin da ya kamata a ce Amurka ta fafata da mu ,a yau ko lamari ya shan bamban. Dabarar da ta rage wa gwamnatin Washington a yanzu, shi ne yunkurin haddasa tsayayya a kasarmu ko ta halin kaka.Ko shakka babu karshen Trump zai zama daya da na Saddam Husain.Saboda shi ma ya yi watsi da yarjejeniyar nukiliya".

 Labarai masu alaka