Girgizar kasa ta sake afkuwa a Papua Gini

An yi gargadi kan yiyuwar afkuwar Tsunami bayan afkuwar girgizar kasa mai karfin awo 7 a kasar New Papua Gini.

Girgizar kasa ta sake afkuwa a Papua Gini

An yi gargadi kan yiyuwar afkuwar Tsunami bayan afkuwar girgizar kasa mai karfin awo 7 a kasar New Papua Gini.

Rahotanni sun ce, girgizar ta afku a yankn New Britain da ke kasar.

Hukumar Bincike Kan Yanayin Kasa ta Amurka ta ce, girgizar ta afku a karkashin kasa da zurfin kilomita 40 a kudu maso-yammacin kauyen Rabaul da ke New Britain. 

Da farin an ce, girgizar na da akrfin awo 7.3 yayinda daga baya kuma aka ce tana da karfin awo 7, ba a bayyana ko ta janyo asarar rai da dukiya ba.

An yi gargadi game da yiwuwar afkuwar Tsunami a yankin da ta afku wanda yake da girman santimita 30. Kuma Tsunamin na iya shafar gabar tekun tsibiran New Gini da Solomon.

A gefe guda kuma, sanarwar da aka sanar a cibiyar gargadi kan tsunami da ke Ostireliya ta ce, gabar tekunkasar ba ta karkashin barazanar Tsunami.Labarai masu alaka