Mutane 12 sun mutu a Indiya sakamakon fashewar wasu abubuwa

Mutane 12 ne suka mutu sakamakon fashewar wasu abubuwa a kamfanin sarrafa bakin karfe da ke kasar Indiya.

Mutane 12 sun mutu a Indiya sakamakon fashewar wasu abubuwa

Mutane 12 ne suka mutu sakamakon fashewar wasu abubuwa a kamfanin sarrafa bakin karfe da ke kasar Indiya.

Labaran da jaridun kasar suka fitar na cewa, lamarin ya afku a wata masana'anta da ke jihar Chhattisgarh inda wasu mutane 3 da suka jikkata suka sake mutuwa wanda hakan ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa 12.

Ana ci gaba da kula da lafiyar mutane 11 da suka samu raunuka.

A gefe guda, an kori daraktan kamfanin tare da wasu manajoji 2.

Tuni aka fara gudanar da bincike kan lamarin.Labarai masu alaka