Rayuwar matar shugaban lnterpol na cikin hatsari

Matar tsohon shugaban ƴan sandar ƙasa da ƙasa wanda aka kama sanadiyar cin hanci da rashawa a kasar China Grace Meng ta bayyana cewar rayuwarta tana cikin hatsari.

Matar tsohon shugaban yan sandar ƙasa da ƙasa Meng Hongwei wato Grace Meng a wani hira da ta yi da gidan talabijin CNN a helkwatarta hukumar yan sandar ƙasa da ƙasa ( lnterpol) dake garin Lyon a ƙasar Faransa ta bayyana cewar tun bayan batar mijinta wasu mutane biyu sun dinga matsa mata lamba inda suke kirar ta ta waya suna mata barazana.

Grace Meng tana kuma kokawa akan cewa wannan ƙalubalen da take fuskanta ka iya shafuwar yaranta biyu.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen China Lu Kang ya bayyana cewar babu bayani a kafafen yaɗa labaran China da cewa wai rayuwar matar Meng Hongwei na cikin hatsari.

A ranar 5 ga watan Oktoba ne hukumar lnterpol ta fitar da sanarwar cewa shugabanta wanda ya taba rike muhimman muƙamai a jami'ar komunist a China ya tafi kasarsa a ranar 29 ga watan Satumba tun a lokacin ba'a ji ɗuriyarsa ba.

A ranar 7 ga watan Oktoba Meng ya bayyana murabus daga shugabancin hukumar lnterpolLabarai masu alaka