Saudiyya ta lalata makami mai linzami da 'yan tawayen Houthi suka harba mamta daga Yaman

Dakarun Kawancen Kasashen Larabawa da Saudiyya ke wa jagoranci sun lalata wani makami mai linzami da 'yan tawayen Houthi suka harba garin Necran daga Yaman.

Kakakin kawancen kasashe Al-Tuki Al-Maliki ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Saudiyya cewa, makaman yaki na sama mallakar kawancen sun lalata wani makami da 'yan tawayen Houthi suka harba daga Yaman zuwa garin Necran.

Maliki ya ce, ba a samu asarar rai ko jikkata ba sakamakon harbo makamin a sama tun kafin ya fado.

Kakakin ya ci gaba da cewa,tun bayan fara rikicin yaman a shekarar 2015 zuwa yau 'yan tawayen Houthi sun kai wa Saudiyya hari da makamai masu linzami guda 204 inda suka kashe mutane 112 tare da jikkata wasu da dama.

A ranar 26 ga watan Maris din 2015 ne Saudiyya ta fara kai wa 'yan tawayen Houthi hari a Yaman bayan da suka yi kokarin kifar da gwamnati zababbiya tare da kwace San'a Babba Birnin Kasar.

Saudiyya na amfani da garkuwar makamai masu linzami wajen harbo dukkan makaman da aka jefa mata dada Yaman.Labarai masu alaka