Mamakon ruwan ya yi ajalin mutane 3 a Faransa

Sakamakon mamakon ruwan sama wanda ya janyo ambaliyar ruwa, mutane 3 sun rasa rayukansu a yankin Aude na kudancin Faransa.

Mamakon ruwan ya yi ajalin mutane 3 a Faransa
Bidiyon yadda ruwan sama ya yi barna da janyo asarar rayuka a Faransa
Bidiyon yadda ruwan sama ya yi barna da janyo asarar rayuka a Faransa

Bidiyon yadda ruwan sama ya yi barna da janyo asarar rayuka a Faransa

Sakamakon mamakon ruwan sama wanda ya janyo ambaliyar ruwa, mutane 3 sun rasa rayukansu a yankin Aude na kudancin Faransa.

Sanarwar da fadar gwamnan Aude ta fitar ta ce, sakamakon ruwan saman kamar da bakin kwarya ya zuwa yanzu mutum daya ya mutu a garin Villardenel inda a garin Villegailhenc mutane 2 suka mutu.

Sanarwar ta kuma ce, gidaje da wuraren aiyuka da dama sun samu matsala inda ruwa ya kai tsayin mita1.5.

Sanarwar ta kara da cewa, a yankin Aude sakamakon ruan sama da iska mai karfi an bayar da sanarwar kar ta kwana. An bayar da hutun makarantu a yankin inda aka kuma gargadi jama'a da kar su fita kan tituna.Labarai masu alaka