ICC ta zuba wa Isra'ila na mujiya

Firaministan Falasdinu, Riyad Al Maliki ya ce,kotun hukunta manya laifuka ta kasa da kasa na gaf da faduwar bakar tasa a idon duniya ganin yadda ta zuba wa Isra'ila na mujiya ba tare da ta ce uffan ba game da cin zalin Falasdinawa.

ICC ta zuba wa Isra'ila na mujiya

Firaministan Falasdinu, Riyad Al Maliki ya ce,kotun hukunta manya laifuka ta kasa da kasa,ICC na gaf da faduwar bakar tasa a idon duniya ganin yadda ta zuba wa Isra'ila na mujiya ba tare da ta ce uffan ba game da cin zalin Falasdinawa.

A ranar Larabar nan da ta gabata ne, Al Maliki ya yi Allah wadai da halayyar da ICC ke ci gaba da nunawa,shakkun ta ke ci gaba da yi na daukar kwararan matakan hukunta Isra'ila da kuma zurfafa bincike kan yawan  Falasdinawa da kasar Yahudu ta ci zalin su.

Da yake bayani a albarkacin babban taron sassa mabambanta na kotun hukunta manya laifuka ta duniya karo na 17, wanda aka shirya a birnin Hague na kasar Netherlands,Minista Al Maliki ya ce tun tun ICC ta fara bincike kan kisan gillar da Isra'ila ke ci gaba da yi wa Falasdinawa amma yadda ta ke jan kafa wajen furta sakamako da kuma ladaftar da gwamnatin Tel Aviv zai sa ta darajarta zubewa a idon duniya.

Al Maliki ya ci gaba da cewa, "Shin yaushe ne za a hukunta Isra'ila ? Ko sai an kashe iillahirn al'umar Falasdinu,ruguje muhallansu, azabartar da yara da mata  da kuma mamaye kasarsu ga baki daya ?

Daga karshe ya ja hankalin shugabar kotun hukunta manyan laifuka ta duniya,Fatou Ben Souda  kan gazawar da ICC game da batun saka wa Falasdinawa, ganin yadda bincike ke tafiyar wahainiya tun shekaru 4 da suka gabata ya zuwa yau,inda ya ce:

"Falasdinawa sun share lokaci mai tsawon gaske suna jiran a kwato musu hakkinsu da kuma hukunta Isra'ila,amma sai shiru kake ji,kamar an shuka dusa.Abinda yasa gwamnatin Tel Aviv ke ci gaba da mamayar Falasdinu salim alim ba tare an dauki wani mataki ba,Kazalika tana ta yi wa shari'a zagon kasa ba dare ba rana.

A watan Disamban shekarar 2014,shugaban Falasdinu, Mahammud Abbas ya rattaba hannu a yarjejeniyar Roma don yin na'am da matakan kotun ICC,wacce kasar ta yanke shawarar zama mambarta a watan Afrilun shekarar 2015.

A watanni tara da suka gabata, Falasdinawan yankin zirin Gaza sun fara yin tsayayya kan iyakar kasar da Isra'ila to samun damar komawa gidajensu a yankunan da ke kan taswirar Falasdinu ta 1948.

Haka zalika sun bukaci da a gaggauta dage takunkuman tattalin arziki da aka kakaba wa Falasdinawa milyan 2 a tsawon shekaru 12,wanda hakan ya tsunduma halin fatara da matsanancin karancin kayayyakin masarufi na yau da kullum.

Tun a ranar 30 ga watan Maris da aka wannan gaggarumar zanga-zangar kawo yau, sama da Falasdinawa 210 ne suka yi shahada,wasu daruruwan dubunnai kuma, suka jikkata sakamakon ruwan harsasai da sojojin Isra'ila suka yi musu.Labarai masu alaka