Ireland ta taka wa Isra'ila birki

Jamhuriyyar Ireland ta kasance kasa daya tak a duk fadin a nahiyar Turai wacce a karon farko majalisar dokokinta ta fitar da dokar haramta wa Isra'ila zaluntar Falasdinawa da kuma mamayar kasarsu.

Ireland ta taka wa Isra'ila birki

Jamhuriyyar Ireland ta kasance kasa daya tak a duk fadin a nahiyar Turai wacce a karon farko majalisar dokokinta ta fitar da dokar haramta wa Isra'ila zaluntar Falasdinawa da kuma mamayar kasarsu.

A yanzu haka dokar wacce aka fitar da ita a makon da ya gabata ta isa kwamitin zartawa ta majalisar dattijan kasar,wacce ake kyautata zaton za ta yi na'am da ita, duk da cewa wasu tsirarrun 'yan majalisu na nuna rashin amincewarsu

Amince da wannan dokar zai sa Ireland ta kasance kasa daya tilo wacce ta taba hawan kan irin turbar, kana ta yi nasara.

Sanata mai zaman kansa na Ireland,Frances Black wanda shi ne mutum na farko da gayyaci jama'a wajen daukar irin wannan mataki,ya wallafa wani muhimmin sako a shafinsa na sada zumunta,inda ya ce: "Wannan abin ta'ajibi ne! Dazu dazu nan aka kammala dukannin matakan sabuwar dokar.Ireland ce kasa ta farko da ta fitar da irin wannan dokar a duk fadin nahiyar turai ta taka wa Isra'ila birki.A yanzu zamu dukufa zuwa takwarorinmu na reshen kasa na majalisar dokokinmu don mu ji ta bakinsu.Ba zamu taba kasa a gwiwa ba wajen ganin mun tabbatar da wannan dokar aikace ba".

Black ya ci gaba da cewa: "Mun yanke shawarar fitar da wannan dokar don ganin kasarmu ta kasance a sahun gaba a jerin kasashen da ke tabbatar da doka da oda da kuma kare hakkokin bil adama ba tare mun kalli fatar jiki ko kuma ra'ayinsa ba.Mamaye kasar da ba taka ba ai tsagwaron sata ne da kuma zalunci.Shin ko yaya zamu ci gaba da rufe idanunmu muna kallon irin wannan rashin adalcin?

Jakadan kasar Isra'ila da ke birnin Dublin ya ce wannan matakin da Ireland ta dauka "Wariya ce ta launi fata" kana "Babbar Hatsari",inda ya ce :"Zamu ci gaba da bin diggigin abin sau da kafa.Zamu kuma mayar musu da martani duba da matakinsu na karshe".

Ireland ta kuduri aniyar daukar wannan matakin tun a watan Janairun bana,amma hakarta ta kasa cimma ruwa,sakamakon wani goron gayyata da kasar ta aika wa jakadan Ireland da ke Tel Aviv,abinda ya sa aka dage dokar har ya zuwa watan Yunin shekarar 2018.Labarai masu alaka