Trump zai aika jiragen yaki Bahar Rum

Gwamnatin Washington ta yanke shawarar aika jiragen ruwa na yaki zuwa yankin Bahar Rum sakamakon kiki-kakan da ya barke tsakanin Rasha da kasar Yukren.

Trump zai aika jiragen yaki Bahar Rum

Gwamnatin Washington ta yanke shawarar aika jiragen ruwa na yaki zuwa yankin Bahar Rum sakamakon kiki-kakan da ya barke tsakanin Rasha da kasar Yukren.

Tashar Talabijin CNN ce ta rawaito wannan labarin bakin wasu manyan shugabannin ma'iakatar tsaron kasar Amurka, Pentagon su 3,inda ta ce rundunar sojin Amurka na shirye-shiryen aika jiragen ruwa na yaki zuwa yankin Bahar Rum.

An dai tabbatar da cewa wannan wata amsa ce ta Amurka ta bayar game da rikicin da ke tsakanin Rasha da Yukren kan matsalar tekun Azak.Haka zalika an sanar da cewa,Pentagon ta bukaci da Turkiyya ta bai wa jiragenta na ruwa na yaki izinin wucewa ta mashigan tekun Bahar Rum duba da yarjejeniyar Montreuil

Kakakin Pentagon,Eric Pahon  ya yi tsokaci kan wannan lamarin,inda ya ce ba zai ce uffan ba game da shirin Amurka na aika jiragen ruwa na yaki yankin Bahar Rum,wanda a yanzu haka ake ci gaba da yayatawa a ko ina,kana ya ce: "Amurka na da cikakken hakki duba da yarjejeniyar Montreuil.Ba zamu bayyana komai kan aiyukanmu na diflomasiyya.

Da yake bayani a gaban maneman kafar yada labarai ta Anadolu Agency,wani babban ma'aikacin gwamnatin Amurka ya ce, rundunar sojojin ruwa na kasarsa ta yanke wannan shawarar don kar a sake a yi ma ta bazata,shi yasa ta bukaci tallafi daga Turkiyya.A tsawon shekaru da dama Amurka ta bukaci  ababen da dama daga hannun Turkiyya,wadanda dukannin su ba su yi hannun riga ba da yarjejeniyar Montreuil.Amma amsoshi kalilan ne da samu daga Turkiyyar.

Bahar Rum za ta kasance sansanin bataliya ta 6 ta rundunar sojojin ruwa na Amurka reshen Turai.

A cewar yarjejeniyar Montreuil  wacce aka rattaba wa hannu a shekarar 1936 kan aiyukan shiga da fice na jiragen ruwa a mashigan Bahar Rum,dukannin kasashen da basu gaba kan tekun za su nemi izini daga Turkiyya mako biyu kafin wucewarsu daga mashigin tekun Santambul.Labarai masu alaka