An ayyana Qudus,cibiyar Islama ta dindindin

Shugaban Hukumar a kyautata ilimi,fasaha da kuma raya a'aldu ta kasa da kasa (ISESCO),Abdul-Aziz bin Osman Tuwaijri ya sanar da cewa an ayyana Qudus a matsayin "Cibiyar al'adu da kuma wayewar Musulunci ta dindindin".

An ayyana Qudus,cibiyar Islama ta dindindin

Shugaban Hukumar kyautata ilimi,fasaha da kuma raya a'aldu ta kasa da kasa (ISESCO),Abdul-Aziz bin Osman Tuwaijri ya sanar da cewa an ayyana Qudus a matsayin "Cibiyar al'adu da kuma wayewar Musulunci ta dindindin". 

Tuwaijri wanda ya yi wani muhimmin bayani a albarkacin taron mai taken "Rawar da Musulunci ya taka a tarihin duniya" wanda Hukumar ISESCO ta shirya a bana a Rabat, babban birnin kasar Morokko, ya ce tuni kasashen Musulmai suka fare aiyukan cude-ni-in-cude-ka don kare kayayyakin Tarihin Islama da ke tsarkakken birnin Qudus.

Haka zalika ya kara da cewa, ISESCO ta ayyana Qudus a matsayin cibiyar al'adu da kuma wayewar addinin Musulunci ta dindindin.

Bugu da kari ya ce,kasashe mambobin ISESCO sun yi amanna cewa, akwai bukatar a gaggauta kare gine-ginen tarihin Islama da ke Qudus musamman ma a yankunan da Musulmai da Yahudawa ke ci gaba da hamayya, ta hanyar ninka aiyuka da kuma tsare-tsaren raya al'adu.

Daga karshe ya ce,ayyana Qudus a matsayin cibiyar al'adun Islama kamar yadda aka yi wa wasu birane gabanin sa, wata hanya ce ta kara dankon zumuncin da ke tsakanin kasashen Musulmai.Labarai masu alaka