Canada ta rungumi 'yar Saudiyyar da ta yi ridda

Shugabannin Canada sun bai wa wata matashiya 'yar Saudiyya wacce ta yanke shawarar kin saka jihabi da kuma juya wa addinin Musulunci baya don rungumar Kiristanci damar cin gaba da rayuwa a kasarsu.

Canada ta rungumi 'yar Saudiyyar da ta yi ridda

Shugabannin Canada sun bai wa wata matashiya 'yar Saudiyya wacce ta yanke shawarar kin saka jihabi da kuma juya wa addinin Musulunci baya don rungumar Kiristanci, damar rayuwa a kasarsu.

A makon da ya gabata ne, Rahaf Muhammad Al Qunun wadda ke kasar Thailand ta tayar da zaune tsaya a shafukan sada zumunta na duniya,inda ta ce tana bukatar tallafin gaggawa daga kasashen yamma saboda idan har ta koma Saudiyya danginta zasu kashe ta.

Wannan lamarin yayi matukar haifar da cece-kuce,inda nan take shugabannin kasashen Yammacin duniya suka dinka furta albakacin bakinsu tare da goya wa matashiyar baya da kuma neman hanyoyin share ma ta kwalba kadaran-kadahan.

Shugaban ma'aikatar shige da fice ta kasar Thailand,Surachate Hakpark ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa,shugabannin Canada sun yi maraba da bukatar Rahaf tare da ba ta damar ci gaba da rayuwa a kasarsu har illa mashallah.

An sanar da cewa, Basaudiyyar mai shekaru 18 da haifuwa za ta je Canada a ranar Jumma'ar nan mai zuwa ta hanyar hawa jirgin saman kasar Koriya wanda zai tashi daga  Bangok ya zuwa Seoul,inda daga bisani za ta doshi kasar ta Canada.

Da yake bayani gaban maneman labaran kafar Reuters, Surachate ya ce: "Canada ta yi maraba da ita,kuma za ta fice daga kasar Tahiland a karfe 11h15 na yamma".

Da aka waiwaiye shi kan batun 'yar kasar Saudiyyar, ministar harkokin wajen Canada Chrystia Freeland ta ce: "Ko shakka babu muna maraba da ita.Amma babu wani karin bayani da zaku ji daga gare mu".

Qunun ta isa Bangok a ranar Asabar din nan da ta gabata karkashin tutar Hukumar 'yan Gudun Hijira na Majalisar Dinkin Duniya, bayan an haramta ma ta shiga kasar tsawon awanni 48.

Matashiyar dai ta zargi danginta da yunkurin ganin bayanta ko ta halin kaka, kana ta ki ta hada ido da mahaifinta da kuma dan uwanta,wadanda suka zo Bangok takanas don komawa da ita Saudiyya.

Wannan matsalar ta sa hankalin duniya ga baki daya ya karkata kan Masarautar Saudiyya ,wacce a yanzu haka yammacin duniya ke ci gaba da gasa wa aya a hannu sakamakon kisan wulakancin da aka yi wa dan jarida Jamal Kashoggi a watan Oktoban da ya gabata da kuma samun ta da hannu dumu-dumu a rikicin kasar Yaman.

A ranar Talatar nan da ta wuce,kasar Australia ma ta nuna bukatar tallafa wa matashiya Qunun.
 Labarai masu alaka