Iraki ta cire Jakada kan yi wa Iran talla

Gwamnatin kasar Iraki ta tirsasa wa jakadanta da ke Iran,Yasin Sherif yin murabus sakamakon tallar da yayi wa wata cibiyar tiyata ta kwaskwarimar gangar jiki ta kasar Farisa.

A cewar sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Iraki ta fitar,"Ministan harkokin waje Muhammad Hakim ya ce an cire jakadan Iraki da ke yankin Meshed na Iran,Yasin Sherif  tare da sake dawo da shi Bagadaza,sakamakon wata talla da ya yi wa kasar Farisa a shafukan sada zumunta".

A tallar an sanar da cewa, Sherif ya gabatar da cibiyar kiwon lafiya ta yankin Meshed inda ya ce ana gudanar da tiyatar gyaran jiki,dashen gashin kai da kula da lafiyar hakora a cikin rahusa.

Tag: talla , jakada , iran , iraki

Labarai masu alaka