Kasar Macedonia za ta sauya suna

Majalisar dokokin Macedonia ta rattaba hannu kan a wani sabon kudurin sauya sunan kasar zuwa "Jamhuriyar Arewacin Macedonia".

Kasar Macedonia za ta sauya suna

Majalisar dokokin  Macedonia ta rattaba hannu kan a wani sabon kudurin sauya sunan kasar zuwa "Jamhuriyar Arewacin Macedonia".

A wani zama na musamman da majalisar mai wakilai 120 ta yi,  'yan majalisu mambobin hadakan kungiyar juyin juya halin na Makedon da na jam'iyyar demokradiyyar kasar Macedonia (VMRO-DPMNE) wadanda dukannin su ke adawa da gwamantin da ke rike da akalar mulkin a yanzu haka ba su hallara ba,inda da sauran takwarorinsu 81 kawai ne suka amshi goron gayyatar da aka ba su.A tashin farko an dai gudanar da zaman a VMRO-DPMNE,inda wassu wakilai 8 masu zaman kansu suka nuna goya bayansu ga wannan sabon matakin da gwamantin Macedonia ta dauka.

Duba da yarjejeniyar Prespa da kasashen Macedonia da kuma Girka suka rattaba wa hannu a ranar 17 ga watan Yunin bara,kaso daya cikin uku na illahirin wakilan majalisar Macedonia wanda ya yi daidai da 'yan majalisu 81 ne suka yi maraba da shawarar sauya suna kasarsu daga "Macedonia" zuwa "Arewacin Macedonia".

An sanar da cewa za a fara aiki da sabuwar ayar dokar da zaran shugban kasar Macedonia Gyorge Ivanov ya rattaba ma ta hannu.

Duk da cewa yawancin kasashen duniya wadanda a ciki har da Turkiyya sun san Macedonia a matsayin "Jamhuriyyar Macedonia",Girka na ci gaba da nuna bukatarta ta ganin kasar ta sauya suna zuwa "Arewacin Macedonia" sakamakon kasancewar wani yankin mai suna "Macedonia" a kasarta.

Tun a lokacin da ta fara cin gashin kanta a shekarar 1991 ya zuwa yau,Macedonia ta kasa zama mambar Tarayyar Turai da ta NATO sakamakon matsalar suna da ta ke ci gaba da fuskanta da makwabciyarta ta kudu,wato kasar Girka.

Shugaban kasar Girka,Aleksis Çipras ma ya yanke shawarar gabatar da irin wannan kudurin a majalisar dokokin kasar a watan Janairun bana.

Duba da yarjejeniyar da suka sun cimmawa,kasashen Macedonia da Girka na son bin dukannin dokoki da kuma ka'idojin da aka gindaya musu sau da kafa,inda daga bisani kuma Macedonia za ta sauya sunanta ya zuwa "Arewacin Macedonia" da zummar zama mambar NATO ta 30.Labarai masu alaka