"Zamu ci gaba da yakar DAESH a Afirka"

Ministan harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo ya ce a sun kammala yakar 'yan ta'addar DAESH a yankin Gabas ta Tsakiya,manufarsu ta gaba ita ce farautar mambobin wannan haramtacciyar kungiyar a nahiyoyin Afirka da kuma Asiya.

"Zamu ci gaba da yakar DAESH a Afirka"

Ministan harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo ya ce a sun kammala yakar 'yan ta'addar DAESH a yankin Gabas ta Tsakiya,manufarsu ta gaba ita ce farautar mambobin wannan haramtacciyar kungiyar a nahiyoyin Afirka da kuma Asiya.

Pompeo ya sanar da cewa, suna ci gaba da ganawa da shugabannin kasar Turkiyya kan batun janye sojojin Amurka daga Sham.

Mike Pompeo wanda ya yada zango a kasar Masar a albarkacin wata ziyara ta musamman da ya yanke shawarar kai kasashen yankin Gabas ta Tsakiya ya yi wata hira a talabijin wannan kasar a ranarsa ta karshe.

A wannan hirar wacce aka wallafa a harshen Larabci,ministan ya ce a ranar Alhamis din nan da ta gabata ya gaba da takwaransa na kasar Turkiyya, Mevlüt Çavuşoğlu ta wayar tarho.

Pompeo ya kara da cewa shugabannin Amurka da Turkiyya na ci gaba da muhawara kan cikakkun bayanai na karshe kan batun janye sojojin kasarsa daga Sham.

Pompeo ya ce wannan matakşn na janye sojoji daga Sham ya zai a daidai lokacin da aka tabbatar da tsaro a illahirin kasar da kuma ganin bayan kungiyar DAESH wacce ta yi kaka yi a Siriya,kana ya ce: 

"Mun kakaba wa kungiyoyin ta'adda tsauraran takunkumai a fannonin da suka jibanci kudi da kuma siyasa.Mun riga mun ga bayan DAESH a yankin Gabas ta Tsakiya.Manufarmu ta gaba ita ce fatattakar 'yan haramtacciyar kungiyar a arewacin Afirka da kuma  Asiya"

Da ya tabo batun kasar Iran, Mike Pompeo ya ce sunaci gaba da kakaba wa Tahran tsauraran takunkumai.

Haka zalika ya ce: "Game da batun yaki da ta'addanci, ra'ayin shugabannin Amurka bai sha bamban ba da na kasashen Qatar,Hadaddiyar Daular Larabawa, Saudiyya da kuma Masar ba.Manufrmu ba yankin Gabas ta Tsakiya kawai ba ne.Burinmu ganin bayan ta'addancin a duk fadin duniya.

Amurka ta bai  tsaro da kuma kwanciyar hankalin yankin Gabas ta Tsakiya muhimmanci matuka gaya kana tana ci gaba da ka-in da na-in wajen ganin ta warware bakin zaren rikicin Falasdinu d Isra'ila da kuma kawo karshen tashe-tashen hankula a yankunan Zirin Gaza da Yammacin gabar kogin Jordan.

Da aka tambaye Pompeo kan ko shugananin Amurka za su halarci taron samar da zaman lafiya a duniya da kawo karshen fitinar Falasdinu da takwarorinsu na Rasha suka kuduri aniyar yi,sai ya ce: "Amurka na a duk inda ake fadi tashin samar da zaman da kwanciyar hankali"Labarai masu alaka