Rana Irin ta Yau 01.01.2019

Muhimman abubuwan da suka faru a ranar 1 ga watan Janairu.

Rana Irin ta Yau 01.01.2019

Rarraba sassan lokaci a mizanin watanni da na shekaru aiki ne na dan adam...Sauran mahalukan da ke doron duniya ba su da irin wannan matsalar.Saboda suna rayuwa ne duba da sauye-sauyen lokuta,daga damana zuwa rani,daga hunturu zuwa bazara.Amma dan adam ba zai taba dogora ba da irin wannan salon rayuwar,sakamakon yadda muke ka-in-da-na-in wajen ganin komai ya bayyana dalla-dalla a matsayin shekara,wata,rana,sa'a da dai sauran su.Wannan yunkurin namu na samun masaniya kan komai ne yasa kankannimu suka samar da kalandoji iri daban-daban wadanda suka fara amfani da su a wasu zamaninnika mabambanta na tarihin bani adama.

Kalandar Miladiya wacce aka fi sani da kalandar Julien,wacce..kawo yanzu ake ci gaba da amfani da ita a kusan illahirin duniya, an samar da ita a miladiya karni na 45.Turkiyya ta ci gaba da amfani da kalandar Hijriyya har ya zuwa shekarar 1925,inda ta sauya alkibla ya zuwa kalandar Miladiya tare da bada..hutun.sabuwar shekara a karo na farko a shekarar 1936.

Mafificin halitta Manzon Allah Muhammadu Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi wanda a shekarar 622 ya yi hijira daga Makkah ya zuwa Madina, ya sake dawowa Makkah a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 630 da wata rundunar soja mai kunshe da sahabbai, 10,000.

An kafa Kungiyar hadakan kasashen Turai a shekarar 1958.

A shekarar 1971,aka haramta tallar taba-sigari a tashoshin talabijin kasar Amurka.

A shekarar 1992,kasashen Turai sun rattaba hannu a yarjejeniyar Schengen da zummar sauwaka shiga da fice da kuma zirga-zirgar mutane da ta hajoji tsakanin kasashen Tarayyar Turai salim-alim ba tare da an gudanar da bincike na kan iyakoki ba.

A shekarar 2002,dokar kawo karshen radadin ciwon majinyatan da ke fama da cututtukan da suka gagari magani, ta hanyar yin allurar guba, ta fara aiki a kasar Holan.Abinda yasa kasar ta kasance ta farko a duniya wacce ta hau kan wannan turbar.

Mu zamu lafiya.Labarai masu alaka