Birnin Istanbul: 13

Barkanmu da warhaka. Bari na fada muku, daya daga cikin abin  da ke sa birnin ya zama na musamma shi ne yadda mutane ke kiran sunansa  da kuma abubuwan dake cikinsa.

Birnin Istanbul: 13

A birnin Istabul kuma, zaka samu daruruwan kayan tarihi da na al’adu a cikinsa. Daya daga cikin wannan kayan tarihi dake garin Istanbul shi ne Kapalıçarşı. Ko wani wuri daga kasashen duniya kake so ka fito, ıdan ka ziyarci Istanbul ba tare da ka tafi kasuwar Kapalıçarşı ba, to ba lalle ne cewa ka ziyarci Istanbul ba. Bayan ka ziyarci birnin Istanbul, to tabbas za ka so ka ba ıyalinka da abokanka labari game da wannan gari kuma a yayin da kake bada labarin zaka yi musu magana game da Kapalıçarşı.

A cikin shirin mu na makon da ya gabata, mu baku labarin kofa daya tak Beyazid meydan wanda ke bude kasuwar Kapalıçarı da abinda Sultan Abdulhamid na biyu a ya bar aka rubuta akan kofar. Saboda haka, yanzu lokaci ta yi da mu baku labari game da kasuwar. Kafin dai haka, bar mu taikata muku labarin kasuwar. Wannan kasuwar shi ne cibiyar kasuwanci kasashen musulman gabas kuma a cikin tsawon tarihi zaka samu irin wannan kasuwa a cikin manyan birane. A kanan garuruwa kuma, za ka samu kasuwarsu yawanci a gefen tituna suke kuma sarakan garin ne ke sa a yi hakan. Wannan kasuwa, tun daga karni na goma sha biyar a lokacin daular Uthmaniya ne aka fara bude shaguna a cikinta. A wannan lokaci shaguna da ake bude wa ana kiransu da suna “Arasta”. Manyan shaguna daga cikinsu kuma, ana ajiye su ne a matsayin cibiyoyin kasuwanci kuma yawanci kayan da ake sayarwa a cikinta mutanen wurin ne suke sarrafasu.

 A yau, ıdan ka je kasashen larabawa da kasar Iran za ka kasuwarsu kamar yadda kasuwan garuruwan Edirne da Bursa na Turkiya suke. 

A yau, Kapalıçarşı ne kakar kowani cibiyar kasuwanci da ba a iya barin zuwa wurin; saboda wannan kasuwa na daya daga cikin tsohuwar kasuwanin duniya kuma a cibiyar Istanbul take.

Asalı ma, kasuwar Kapalıçarşı na daya daga cikin abinda ya bar birnin Istanbul ya yi suna. A nan ne mutane da dama suka kafa shaguna kusa da masallacin Ayasofya domin neman arziki a zamanın Bizans. Amma kasuwar Kapalıçarşı  kuma Fatih Sultan Mehmed ne ya bar aka fara ginawa a shekarar alif dari hudu da sittin da daya.

Dalilin da yasa Fatih Sultan Mehmed ya bar aka kafa kasuwar Kapalıçarşı shi ne, bayan da daular Uthmaniya suka yi nasarar birnin Istanbul, sai ya sa aka gina kasuwar domin ya janyon hankalin makota kasashen musulmai. A cikin wasu ‘yan lokuta ne sai aka kare ginin. Saboda girgizar kasar da suka faru a kasuwar Kapalıçarşı ne ya sa aka yi masa wasu canje-canje. Wannan shi ne ya sa a yau za ka ga kasuwan a haka. Kasuwar Kapalıçarşı wurin ne da kowani mutum ya kamanci ya ziyarci a lokacin da ya tafi birnin Istanbul.

A zahiri ma, kapalıçarşı kadai zai iya zama gari. Saboda idan ka duba fadin girman wurin a gefe guda kuma irin yawan shaguna dake cikinta tare da adon da aka yi wa wurin zaka fahimci hakan. Saboda kamar yadda muka fada muku a cikin shirinmu da ya gabata, fadin wurin ya kai akalla mita dubu talatin da dari bakwai inda akwai tituna guda sittin a cikinta. Kuma shaguna fiye da dubu uku da dari da shida baya ga haka akwai masallatai biyar, makaranta daya, popon ruwa bakwai, rijiya goma, kogi daya, kananan  kofofi goma sha takwas da kuma ofisoshi guda arba’in a cikinta. A gefe guda kuma rijiyar da tafi kowaci kyau a duniya wato “altın işlem” da ga cikin kasuwar take. Saboda a duniya wannan rijiya babu irinta kuma an kewaye ta ne mutum mutumin mata. An yi wannan ne domin nuna yadda mata suka taka rawar gani wurin ganin cewa a gina rijiyar.

Kapalıçarşı a kowani lokaci akwai mutane cike a cikinta. Irin yawan mutane dake ziyarar manyan kasuwar duniya da na Turkiya a cikin wata daya, irin wanan yawa ne ake samu a rana daya a cikin Kapalıçarşı. Kusan mutane dubu 36 ne ke aiki a cikin wannan kasuwa: kuma a lokacin rani kusan mutane dubu dari biyar ne ke ziyarar wurin, a lokacin sanyi kuma kusan mutane dubu dari uku ne ke ziyarar kasuwar. A wurin ne za ka samu kayayyakin al’dun Turkawa da dama, a cikinsu har ma da kafet da ake saka.

A cikin kasuwar Kapalıçarşı, akwai wani bangare da ake kiransa da suna Eminönü. Wannan shi ne daya daga cikin gadon daular Uthmaniya. Saboda haka kungiyar dilallan raya al’adu na shekarar dubu biyu da goma ta saka wurin a cikin ayyukanta. Kungiyar dilallan raya al’adu na shekarar dubu biyu da goma za ta sake gyaran wurin ne domin ta kara ba mutane sha’awa. Wannnan shi ne dalilin da ya sa daraktan kungiyar dilallan raya al’adu na shekarar dubu biyu da goma ya ba da umarnin cewa a fara gyare-gyaren daga bangaren Eminönü domin muhimmancin da wurin ke da shi a cikin tarihi. Dalilin da yasa kungiyar ke wannan aiki shi ne, nunawa duniya yadda kyawon wurin ya ke. Daya daga cikin manufansu kuma shi ne sunan wanan kasuwa ya shiga cikin jerin kayan tarihin hukumar kula da ilimin kimiyya da raya al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO.Labarai masu alaka