Birnin Istanbul: 14

Barkanmu da warhaka, da sake saduwa a cikin a shirin na mu na birnin Istanbul. Ku biyo mu don jin me shirin mu wannan mako ke dauke da shi.

Birnin Istanbul: 14

Akwai alamomi da dama da ke sa gari ya zama na musamma. Garuruwan  da suka shahara a duniya ko a nahiyoyi suna da alamar da ake ganesu da shi. Hasumiyar Galata na daya daga cikin wani alamar da kungiyar dillalan raya al’adu na shekara dubu biyu da goma ya suka ya  zama a matsayin alamar birnin Istanbul. 

A shekarun baya ana kiran birnin Istanbul da Byzantiyom, daga baya kuma Konstantinopolis; daga kudancin birnin akwai tekun Marmara daga bangaren gabas kuma mashigar ruwa ta teku, a bangaren arewa kuma akwai mashigar ruwa ta teku, a bangaren ne akwai wani wuri mai suna Haliç wadda ke kan wani tsibiri na tarihi. A gefen Haliç wanda aka fi sani da suna ‘Golden Bridge’ zaka ga hasumiyar Galata wanda shi ne daya daga cikin alamomin birnin Istanbul. A cikin hasumiyar Galata ne aka samu Galata; wannan Galata wuri ne da mutanen Byzantiyom suka gina bayan sun samu ‘yanci daga Ceneviz a shekaru dari biyu da suka gabata. Har kafin daular Uthmaniya suka yi nasarar birnin Istanbul, an gina hasumiyoyin guda ashirin da hudu saboda birnin su kara girma; dukkan wannan hasumiyoyi, hasumiyar Galata ce wanda ta saura a yau.

Hasumiyar Galata na daga cikin gatangu mafiya tsayi da mutanen Ceneviz suka gudanar lokacin mulki Galata a shekarar alif dari uku da tamanin da hudu. Wannan hasumiya mutanen Ceneviz sun gina ne domin tsaron kansu, a lokacin daular Uthmaniya kuma sai dakarun da ake kiransu da suna Yeniçeriler suka fara anfani da wurin. A cikin karni na 16 kuma wurin ne aka yi anfani da shi a yaki. A lokacin sarki Selim na biyu a zamanin daular Uthmaniya, sarkin ya bar masu gine-ginen kasar Turkiya suka yi wa wurin kwaskwarima saboda a dinga anfani da shi. Bayan haka kuma a lokacin Sultan Mustafa na biyu, sai babban malamin daular Uthmaniya Şeyhülislam Feyzullah Efendi tare da Papa Cizvit suka hada kan wurin kiyaye Galata. Amma sai dai dukkan kokarin da suka yi sun kawo karshen kula da wurin ne a shekarar alif dari bakwai da uku. A cikin karni da 18 kuma, sai aka bar hasumiyar Galata ta zama wuri da aka ajiye Mehter ya bada labarai a cikin dare. A shekarar alif dari takwas da saba’in da bakwai ne aka fara anfani da hasumiyar a matsayin wurin bada labari da kuma wuri a lokacin da goba ta kama. A lokacin Bizantiyom sun mayar da wurin a matsayin babban alamarsu, a lokacin  mutanen Ceneviz kuma suka mayar da wurin a matsayin hasumiyar annabi Isa sai kuma a lokacin daular Uthmaniya kuma sai suka yi wa wurin wasu canje-canje.

Sanadiyyar gobara da ta kama a cikin karni  da 17, shi ya sa aka ajiye  wani kalangu mai suna Kös a hasumiyar Galata saboda kowa ya samu labarin wannan gobaran. Kös, wani babbar kalangu ne da Mehter ke anfani da shi wurin sanarwa. Saboda girman wannan kalangu ne ya sa idan za a je yaki a lokacin daular Uthmaniya sai a daura su akan doki ko kuma kan jaki. Wannan kalangu yawanci, mutane biyu ne ke kadawa kuma idan an kada, mutanen dake nisa ma za su iya jin sautin.

Wannan wurin da ake anfani da shi wuri bada labarin gobara, gobara ta kamata a cikin wasu ‘yan lokuta. A madadin ta sai Sultan Mahmud na biyu ya bar aka gina wata sabon hasumiya wadda ke dauke da gatangu guda hudu tare da dakin ibada da kuma wasu dakuna. Sai dai, a cikin karni na 19 kuma gobara ta sake gama wurin. Wannan shine ya sa aka sake yi wa samar hasumiyar kwaskwarima. Wannan karo a shekarar alif dari takwas da saba’inda  biyar, sai wata ambaliyar ruwa ya ruguje wani bangare daga cikin hasumiyar. Dukkan wannan kasada da ta faru ga hasumiyar Galata, a tsakiyar shekarar alif dari tara da sittin sai aka yi mata wata babban kwaskwarima.

Ana tunanen cewa a yau girman hasumiyar Galata kamar na lokacin Ceneviz ne. Idan ka tsaya daga Halıç, nisansa mita dari hudu da ashirin da biyar ne kuma tsawonsa mita talatin da biyar.  Da yake gyare-gyaren da aka yi a shekarar alif dari takwas da talatin da biyu a lokacin sarki Mahmut na biyu ne wannan shi ne yasa idan ka kaje Galata, za aka rubutu da sarkin ya yi. Bayan  hawa na hudu a cikin hasumiyar akwai barandan da ya fi kowani girma inda idan ka saya wurin za ka ga wurare daban-daban. A hawa na takwas akwai labule masu fadi, a hawa na tara kuma akwai labulen da ya fi kowani girma kuma ya ke jan hankalin mutane. A kudancinta akwai wani kofa wanda ke bude  wani babban rami. Bisan matattakala mai aikin da lantarke kuma akwai zane-zanen Matrakçı Nasuh wanda ya rubuta a ashekarar alif dari biyar da talatin da biyu a zamann Sarki Muhteşem Süleyman a lokacin daular Uthmaniya. A hawa na bakwai kuma, akwai mutum mutumin Hazerfen Ahmet Çelebi. To masu sauraro tunda mun kai har nan, zamu so mu baku labrin game da Hazerfen Ahmet Çelebi.

Hazerfen Ahmet Çelebi, yayi rayuwa a cikin karni na 17 a birnin Istabul a lokacin daular Uthmaniya kuma shi ne mutum da farko da yayi fiffike dake tashiwa a sama. Masana tarihi sun bayyana cewa, Leonardo Da Vinci da kuma babban malami İsmail Cevheri wanda yayi rayuwa a cikin karni na goma sun karbi ilhaama game da kera jirgin sama ne ga wannan mutumi. Da farko Hazerfan ya fara bincike game da yanayin iska sa’anan sai ya kera fiffike biyu daga katako inda yayi mata gwaji daban-daban domin ya ga ta tashi sama. A karshe dai, a shekarar alif dari shida da talatin da takwas sai ya hau samar hasumiyar Galata inda ya sake kafadun daga sama. Wannan kafadar ya yi tafiya daga gadar teku inda ya wurin yankin Anatolia har zuwa unguwar Üsküdar. Wannan al’amari ya jawo hankalin mutane. Wannan shi ne ya sa da Murat  na hudu ya ga wannan aiki, sai daga baya sai ya gana da Şeyhülislam domin neman shawara. Hazerfan ya yi hijira zuwa kasar Algeria har sai da ya ci shekaru 31 a wurin sa’anan ya dawo. Bayan ya dawo sai wasu mutane daga Turai suka nuna muhimmanci abinda ya yi wannan shi ne ya sa sai ya sake sabon gwaji a Ingila. A yau, sunansa ne aka sakawa daya daga cikin filin tashin jiragen saman Turkiyya.

Idan kana son ga ka kyawon birnin Istanbul da kuma yadda teku ya raba garin biyu, rabin na yankin Asia inda rabi kuma ke yankin Turai to lalle sai ka hau bisa kan hasumiyar Galata. Ko da yake a da, hasumiyar an yi anfani  da su saboda dalili daban-daban amma  a yau, ana fani da wurin ne domin ganin yadda kyawon birnin Istanbul yake. A karshen hawan hasumiyar, ana anfani da su a matsayin kantin da kuma gidan nishadi. Wannan wuri da kuma filin panorama wuri ne da mutum ba zai iya barin kallonsu ba.

Saboda anan ne mutum zai samu yanayi mai kyau tare da sauraron wakoki Turkiya,  raye-raye da kuma nune-nune, asali ma idan kana son jin dadin rayuwa sai ka zo a wurin dara dare.

Masu sauraro anan muka kawo karshen baku labarin hasumiyar Galata;  mu hadu a mako mai zuwa domin mu baku labarin wata sabuwan hasumiya mai suna Kız Kulesi wanda ke dauke da wani labari soyayya mai muhimmanci a cikin shekaru dari da suka gabata. kafin mako mai zuwa  TRT hausa ke cewa ku huta lafiya.Labarai masu alaka