Cigaban Tattalin Arzikin Turkiyya: 13

Barkanmu da sake saduwa a cikin wani sabon shirin cigaban tattalin arzikin kasar Turkiyya.A shirinmu na yau zamu tabo batun lamurran da suka danganci bashi da kuma rawar da bankuna da suke takawa a tattalin arzikin kasar Turkiyya.

Cigaban Tattalin Arzikin Turkiyya: 13

A kasashe masu ci gaban tattalin arzikin bankuna na taka muhimmiyar rawa a wajen bunkasa tattalin arziki. Domin suna amfani da kudaden da suka karba daga hannayen masu hannu da shuni da kuma wadanda suka tanadi arzikin da yawan sa ya wuce bukantunsu,domin ba wa mabukata a matsayin bashi.A tsawon shekaru 300 da duniya ta ci gaba da kasancewa a karkashin wannan tsarin kudi,bankuna sun bayar da gudunmowa haikan a wajen bunkasa tattalin arzikin duniya.

A kasashen da shirin ya samu gindin zama,al'umomi na samun damar daukan bashi ,inda suke biya ta hanyar bada kudin ruwan da bai taka kara ya karya ba.Abinda yasa masu hannu da shuni suke cuncurundo a ire-iren wadannan kasashen domin zuba jari mai yawan gaske.Yawan kudaden da masu hannu da shuni za su zuba a kasa,yawan ci gaban da za a samu a harkar tattalin arziki.Tun bayan karyar tattalin arzikin da ta jefa duniya a cikin halin ha'ula'i,bankuna sun nuna wa duniya irin rawar da suke iya takawa domin hana irin wannan matsalar ta sake afkuwa.Duk kasar da ke son ta samu cigaban tattalin arzikinta,to dole ne ta tanadi ingantaccen tsari kudi da kuma kyaukyawan yanayi domin tafiyar da harkokin ajiyya da kuma juya kudade a bankuna.

Tun a shekarar 2011 kasar turkiyya wacce ta kafa wa kanta manufar habbaka arzikinta,ta sake fiddo da sabbin tsare-tsare a sha'anin kudi da kuma bankuna,inda ita ma ta sauya numfashi a wannan harkar kamar sauran takwarorinta na duniya. Domin tabbatar da doka da oda a  wurin tafiyar da tsare-tsare da ta samarwa kanta,Turkiyya ta kafa hukumar BDDK mai manufar sa ido, warware karyar darajar kudi da ma dukkanin matsalolin da suka jibanci kudi da kuma bankuna.Tun kafuwar wannan hukumar a shekarar 2008 kawo yanzu,komai na tafiya dai-dai ba tare an fuskanci wata matsala ba,inda BDDK take ci gaba da zama tushen jawo hankalin dubban masu hannu da shuni na turai da ma sauran sassan duniya.Idan aka dubi yadda karyar tattalin arziki ta girgiza kasashen duniya musamman ma na nahiyar Turai ,ana iya cewa lamarin bai haifar da yawan asara ba a Turkiyya.

A cewar bayanan da aka samu daga babbar hukuma mai kula harkar kudi da Bankuna a kasar Turkiyya,a shekarar 2001 bankunan kasar sun juya makudan kudaden da yawansu ya haura kusan dalar Amirka bilyan 11,a yayin da shekarar 2015 kuma suka tanadi kusan tiriliyan 1 na dalar Amirka.Bankunan bunkasa tattalin arziki kuma a shekarar 2011 sun bayar da bashin da yawansa ya haura dalar Amirka bilyan 1,a yayin da a shekarar 2015 suka bada bashin zunzurutun kudi akalla dalar amirka bilyan 13.Illahirin wadannan bankuna na bayar da kudi ne a karkashin ingantattun ka'idoji da kuma dokoki,inda wadanda suka dauki bashi ke biya kashi 3.1 na yawan kudaden da suka karba a matsayin kudin ruwa,a yayin da a kasar Girka ake biyan kashi 34.3 a matsayin kudin ruwa,a kasar Portugal kashi 11.2 sannan a Faransa kuma kashi 4.5.Wannan matakin da kasar ta dauka na da muhimmanci sosai a wajen dakile matsalar karyar tattalin arziki da kuma dukkanin matsalolin da ke iya gurgunta lamurran bankuna.

A nan ne za mu dasa aya,a madadin wanda ya rubuta wannan shirin wato Dokta Husain Karameklı malami a tsangayar tattalin arziki na jami’ar karabuk.Ni da na karanto Muhammed Ali, na ke cewa da ku mu huta lafiya.  Daga TRT hausa Muryar Turkiyya.

 Labarai masu alaka