Gudunmowar Musulmi a Duniyar Kimiyya: 13

Allurar ido mai tsawon  milimeta 130

Gudunmowar Musulmi a Duniyar Kimiyya: 13

Karfen karkare  datti  hakora ko Raspatar mai tsawon milimeta 110

Na’urar daidaita doron baya

Kadan kenan daga  wadansu  kayayyakin aikin da musulmai masana kimiyya su kayi zaman amfani da su a shekaru dubu da suka wuce.

A yau cigaban da a ke dashi a fannin  kiyon lafiya ya dauko asili daga  aiyukkan wadansu fitattun masan biyu watau ibn sina da kuma ez zehravi. Hasali ma, Rubuce-rubucen da zane-zanen da wadannan masanan suka yi a cikin litattafai a wancan zamani ne,  likitocin kudancin  turai suka yi amfani domin habakar kiyon lafiya a turai.

Almakashin da a yau ake amfani da ita a fannin tiyata a asibitoci da dama ya dako asali da ga wani almakashi mai lebe wanda khalifa al halabi ya kera. Kuma a lokacin da ya kera wannan almakashin ne domin rike yankunnan idanu masu ciwo.

Wadansu daga kayan aikin da Halebi da ya yi amfani da su a fannin kula da ido su ne:

Almakashi mai cire ciwo daga tushen sa mai zagayayyen baki.

Makarkarin kurajen jiki da kuma dattin hakora mai sunan Mijrad

Almakashin da ake amfani da shi domin cire duk wani  abinda da ya rufe ido.

A wancan lokacin a samun babban cigaban ne,  domin mulsulmai masana sun yin amfani da kayan aikin wanda sukayi fice sosai . Ez Zehravi, shi ne wannan masanin  kiyon lafiya na farko wanda ya rubuta liffatafai tare yin zane-zane masu bada bayani bisa kan komai,  gabanin ma  zamanin sabon karni a turai.

A miladiya karni na goma masani Zehravi yayi amfani da wani kayan  aiki mai sunan Koter. Wannan kayan aikin  yayi amfani dashi ne domin waraware duk wata matsala da ta shafi cikin kunne.

A cikin kayan aikin da musulmai suka yi zaman amfani da shi, kuma wanda har yanzu baya da wani mai kama da shi a fagen asibitocin turai shine Neshter. Neshter dai wani harsashe ne mai lankwasa wanda a cikin sa wata reza ke boye . Rezar tana iya fitowa kuma tana iya  komawa a cikin Nester din ba tare da wata matsala ba,  kuma duk wani lokacin da  ake so. Ta hakan ne marar lafiya mai ganin rezar da ke boye.

İdan muka la’akkari cewa an yi amfani da wannan irin kayan aiki a zamanin da ba a aiki da allurar kashe gaban jiki domin yin tiyata,  sai mu ce Neshter dai wani kayan aiki ne wanda ya kawo gudunmowa sosai wurin kwantar hankali wadanda a ke wa tiyata..

 

 

 Labarai masu alaka