Gudunmowar Turkiyya ga Kasashen Waje: 13

Barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa damu don jin shirin GUDUNMOWAR TURKIYYA GA KASASHEN WAJE. A yau zamu tattauna gudunmowa musamman ruwan sha da Turkiyya ta isa da su a nahiyar Afirka dangane da bukukuwar ranar ruwa na kasa da kasa a duniya..

Gudunmowar Turkiyya ga Kasashen Waje: 13

A ranar 22 ga watan Maris ne aka gudanar da bikin ranar ruwa na kasa da kasa inda dukkkani kasashen duniya suka gudanar da nasu bukukuw na musamman.Wato abin lura shi e duk da yawan ruwa wadda ta yi wa duniya zobe, har wayau akwai gurare da babu ruwa. A Turkiyya dai kungiyar bada agaji TIKA ne ta taimakawa wasu kasashen nahiyar Afirka wadanda babu ruwa.kamar yadda muka saba a shirinmu, a yau zamu tattauna lamarin tare da Selahatin Bostan na kungiyar bada agaji Turk Kizilay .....

Ga fadar wani mai gine gine ya ce Turkawa sun yi yunkurin kwace Tsakiyar Asiya ne karkashin Oğuz Kağan da ya rinka cewa idan aka ci nasarar teku, da haka za a samu kifaye yadda ya kamata. Oğuz Kağan dai ya nuna karfinsa gurin fadada yankin Turkiyya da Turkawa baki daya ta hanyar tekun tsakiyar Asiya.Da haka ne aka samu wasu ‘yan gudun hijira a guraren inda kuma aka fuska nyunwa a lokacin. Don haka ne aka ce wadanda suka ki ruwa sun ki wayewa domin ruwa ne tushen komai.Don haka kafin a samu wayewa kamata ne a samu inda ruywa ya ke.  A tarihin Turkiyya dai Oğuz Kağan ya shahara sosai. Shine ya fadada guraren yankin Ege, Akdeniz da kuma Marmara karkashin Daular Uthmaniya. Tun tattabakunnin Uthmaniyawa ne aka fara koyon wayewa. Turkawa ne suka fahimci menene ainihin wayewa. Sun gano hakan ne da kwace yankin da akwai ruwa. A nan ne suka isar da shi a kasashe da dama. Sun kafa gurare don isar da ruwa a guraren.Wannan ilimin wayewa  Ubangiji ne ya yi wa Turkiyya wannan baiwa. Ni’ima ne daga gareshi.Wannan ruwa da kowa yake amfani da shi daga ilimin Turkawa ne aka samu.Haka zalika manoma kuma ke amfani da su har ila yau. Don haka aka ce idan dan’uwwa ko kuma makwabta na cikin halin kunci, tilas ne a taimaka.

A ranar 22 ga watan Maris shekarar alif dari tara da tisin da tara ne Majalisar Dinkin Duniya ta fara gudanar da bikin ranar ruwa na kasa da kasa. Wato Worlds Water Day a turance. Kusan shekara ashirin da uku kennan tun da aka fara gudanar da abu irin haka. Kowace shekara ana shirya aikace aikacen isar da ruwa inda babu.  Majalisar Dinkin Duniya ta yi bincike inda ta ganıo cewa a duniya a yau,har ila yau  mutane biliyan 1 basu samun damar ruwan sha mai tsabta. Haka kuma ana ci gaba da samun matsaloli irin haka yau da kullum. Tun abinda ya dauki yara kanana, mata da maza suna cikin halin kunci don rashin ruwa wato mutane sama da miliyan 2 basu da ruwan sha,cikakken kiwon lafiya da kuma kamfar ruwa.  Da ya kamata a ce ruwa ta isa kowa a ban kasa amma inaa.Ba a cimma burin haka ba domin bamu taimakawa juna.Ruwan da gagarumar kasashen duniya ke batawa ya isa ya ciyar da nahiyar Afirka baki daya. Turkiyya dai na ci gaba da yin gwargwadonta gurin aika taimako a musamman ciki har da ruwa a kasashen da babu.TİKA kungiya daya daga cikin kungiyoyin  bada agaji na Turkiyya ne ta isar da wannan taimako a nahiyar Afirka. Haka zalika ta rinka isar da gudunmowa a nahiyar Asiya, kasashen Balkan, da kuma tsakiyar Asiya don su samu damar gudanar da aikşn noma yadda ya kamata da kuma sha haka zalika zasu samu damar gudanar da wayewa yadda ya kamata.

Nahiyar Afirka ta shekara tana fuskantar kamfar ruwa rashin ruwan dangane da tsarin yanayin kasarta. Da kuma hayaniyar siyasa da ta yi sanadiyar wargaje tsari da aka kafa. Dalilin haka yasa miliyoyin mutanen Afirka basu da  ruwa mai tsabta. Tun da aka kafa ita TİKA wato ta isa kusan dukkanin kasashen Afirka gurin isar da taimako. Tun abinda ya dauki gabashin zuwa yammacin har da arewa da kuma kudancin Afirka.  TİKA, ta gina rijiyoyi sittin da hudu a  Moritanya, goma a , Sengal, talatin da shida a  Mali dari da hamsin da bakwai a Nijar, takwas a Gambiya,, sabain da hudu a Burkina Faso, ashirin da biyar a Somaliya,goma a Kamaru, talatin da biyar a Sudan, biyu a Gabon, biyar a Malawi wato akalla ta gina rijiyoyi dari biyar da sabain da takwas a nahiyar Afirka. Miliyoyin mutane ne ke sha suna amfani da ita suna samun damar fitar da najasa daga garesu.Kuma kodayaushe zasu rinka godewa Turkiyya domin tausaya musu da ta yi. Ba nahiyar Afirka kadai TİKA ta isar da taimakon ba, ta je Gabas ta Tsakiya, inda ta yi fabon jama’a sama da miliyan gurin samun ruwan sha.TİKA ne ta gyara abubuw ada suka bata a  Beyt Lahiya, Deyr El-Balah, Han Yunus da kuma harkokin jin dadin al’umma.Guraren ma dama suna tsawon ramuka sama da dubu 5 a karkashin kasa inda aka tono ruwa.

TİKA ne ta gyara rijiyoyi sama da goma sha biyar da suka yaki ya rugurguje sama da tsawon kilomita ashirin da biyu. Haka zalika a Gazan kuma aka gyara gurin samun gishiri ta kuma sake gina makarantu dari uku da arbain kuma adalibai yara kanana sama da dari shida 600 ne ke amfani da wannan ruwa a makarantu. Kodayaushe suna yiwa Turkiyya adu’a. A tsakiyar Asiya da kuma Yankin Balkan kuma nan gaba za ta fadada harkokinta.

Na’am da farko mun fara da cewa Ruwa ce Wayewa. Na2am haka ne babu shakka. Don haka Turkawa ko kum gwamnatin Turkiyyaa kodayaushe za ta rinka taimakawa kasashe masu halin kunci sanadiyar rashin ruwa.

Mun dasa aya a nan. Mu hadu a mako mai zuwa don ci gaba da jin shi,rin Gudun mowar Turkiyya ga kasashen waje.Labarai masu alaka