Gudunmowar Turkiyya ga Kasashen Waje: 14

Barkanmu da yau da kuma sake saduwa damu don jin shirin GUDUNMOWAR TURKIYYA GA KASASHEN WAJE daga nan TRT Hausa.

Gudunmowar Turkiyya ga Kasashen Waje: 14

 A wannan mako zamu tattauna tallafin karatu wato Scholarship ko kuma  Bursları a turkance da Turkiyya ta bawa dubunnan daliban kasashen waje. Haka zalika zamu tattauna yadda kasar ta samu matsayin cibiyar dalibai a duniya. Ba da bata lokaci ba, zamu tattauna bayanai da  Selahattin Bostan na kungiyar bada agaji ta Turkiyya Turk Kizilay ya yi game da batun.

Idan aka ambaci wata kasa ko kuma wata daula a matsayin daula mai iko me ake nufi? Wannan tambaya sau da yawa a kan yi ta a sharhin al’amuran duniya. Sau daya idan an yi wannan tambaya kuma wato a fannonin neman ilimi ne ake samun jawabi. Kafin kasa ko kuma Daula ta zama mai iko da kuma girma akwai sharudda da dama da ya kamata ta bi. Wata a kan harkokin tattalin arziki ne ta ke zama babba, wata kuma karfin sojinta, sai wata kuma a tarihince, sai kuma wata a fannin kirkiran wasu dabaru.

Wato ita tambaya da muka yi amsoshinta bashi a nan na zamaninta, sai an duba tun tarihin da’. Akidojin wayewa, masana, manazarta, da sauransu. Idan an dauki tarihin tun a da, to lalle za a samu ainihin cikakkun bayanai game da tsarin kasa, ikonta da kuma  yanayinta.  A wani lokaci kasar China ne ta zama kasa mai babbar iko, a wani lokaci kuma Girka. Amma idan an taho a daular Uthmaniya sai a gano cewa ta zauna tana ikon duniya shekara da shekaru. İnda ta rinjaye abubuwa da dama. A lokacin ne aka samu jaruman kwaron zane da suka fi kowane a duniya a daular, A yau a Amurka mutun mutunin Liberty da take takama da shi  an yi ta ne karkashin jagorancin Sarkin  daular Uthmaniya. An yi irin haka a mutun mutunin  fadar Galata, Gadar da sauransu. Sojin daular kuma ta yi nata kokari don karfafa ikon daular, wato a nan ne aka fara tunanne sake tsarin kasar  inda wasu kuma suka isa kasashen waje.

Amurka ce kasa wadda ta hada masanan duniya don samun iko. Har ma ‘yan kasar Indiya masu kokarin manhajar kwamfuta suna isa Amurka da liminsu na kwamfuta. Idan suka je kuma basa dawowa kasarsu. Likitocin Turkiyya da dama kuma suna isa Amurka don gudanar da gwaje gwajen gano cututtuka. Wato Amurka dai cibiya ce na masana da al’umma da dama. Don haka ta zama kasa mai iko da kuma karfi a duniya domin karfafa masana.Turkiyya kuma kasa ce wadda ta samu sakiya gurin tsarin kasarta. Bayan rushewa  daular Uthmaniya ne Turkiyya ta sake farfadowa daga rikice rikice. A yanzu tana gwagwarmayar zama cibiyar dalibai a duniya.

A da gwamnatin Turkiyya ce ke aika dalibanta a nahiyar Turai don koyon karatu amma a yanzu daliban Turai ne ke isowa Turkiyya  wato abun ya canza. Kungiyoyi da sauransu sun fara bada tallafin karatu wa dalibai.  Hukumar kula da harkokin Turkawa a kasashen waje da kuma bada tallafin karatu YTB ne ta fara gudanar da hakan. Dalibai a kowane kasa na sanya hannu tahowa Turkiyya don karatu.Ga bincike da ita hukumar ta yi, ta gano cewa a duniya kasashen Amurka,  Ingila, Kanada  saanan Turkiyya ta biyo wato gagarumar kasashe masu bawa dalibai tallafin karatu.

A bana shekarar 2016 an bude shafin yanar gizo don daliban kasashen waje su sanya hannu tun a ranar 29 ga watan Fabrairu. Inda gwamnati ta kebe kudi  don kula da su daliban da zasu ci nasarar tallafin sama da dubu 200. Haka zalika zasu yi karatun  yaren Turkance  shekara daya ba da biyan ko kobo ba, sai su isa jami’ar da suka zabi,haka zalika za a basu tikitin jirgin sama zuwa da komawa kasarsu idan sun kammala karatu. Suna samun kudin allawas a kowace wata, gurin barci,inshora na kiwon lafiya, da sauransu. A shekarar 2015 dai dangane da wadanda suka iso Turkiyya don karatu ne yasa kasar ta zama cibiyar dalibai a duniya, amma bana ba a fitar da wadanda suka ci nasarar tallafin ba.

Akalla akwai dalibai sama da dubu 70  a Turkiyya wadanda suke kan tallafin karatu. dubu 15 daga cikinsu gwamnatin Turkiyya ne ke taimaka musu kai tsaye. A shekarar 2015 dai dalibai daga kasashen waje dari da tamanin da biyu 182 suka iso Turkiyya. Wato kowane dalibi na sha’awar zuwa Turkiyya don karatu. A shekarar 2011 daliban kasashen waje  dubu 8 ne suka sanya hannu. Sai a yanzu aka samu daliban kasashen waje dubu  tisin da biyar. Ana sa ran cewa  bana alkalumar zasu dadu matukar daduwa.  Wayewa da kansa ta dawowa inda aka fara gudanar da ita. A yau masanan gine gine da kwararrun manazarta daga kasashen Kolombiya, Filipin, China, Spaniya,  da sauransu suna sha’awar tahowa Turkiyya don ci gaba da karatu da nazari. Ba wai tattallin arzikin kasar Turkiyya ya fi na kowace kasa ba, amma abun da ya kamata a lura shi ne, al’adun Turkiyya da yadda ya yadu a duniya. Wato kowane dalibi da zai taho Turkiyya karatu yana zama ne mai girmama mutun kuma yana samun dabi’u masu kyau. A yau idan dan Turkiyya ya je nahiyar Afirka ya yi yarensa sai ya ga cewa dalibai da dama zasu fahimci abun da ya ke nufi domin dayawansu sun iso ne a Turkiyya. Idan dan Turkiyya ya yi tambaya domin yana mamakin ta yaya dan Afirka ya ke yaren turkanci, sai ka ga cewa dalibin ya ce , ai ni na zauna Turkiyy a Isstanbul ne na yi karatun digirin  tibbi, likitanci, ko kuma siyasa ne na koyi a jami’ar Ankara. A nan ne ikon kasa ke yaduwa a fadin duniya baki daya.  Don haka za mu dasa  aya a nan, muna fatan kowa zai yi wa Turkiyya a du’a kuma ya godewa hukumar gudanar da hakan.

A gaishe ki Turkiyya !!!Labarai masu alaka