Kundin Hikima:13

Barkanmu da sake kasancewa a cikin wani shiri na Kundin hikima, wanda ke kawo muku bayanai game da rayuwar wasu mutane da suka rayu a yankin Anatoliya, kuma suka sadaukar da kai wajen taimakon al‘uma.

Kundin Hikima:13

A miladiya karni na goma sha biyu , Garin Belh wanda  yake a arewacin  kasar Afganistan,  ya kasance  daya daga cikin manya-manyan cibiyoyin al’adu na duniya. Wannan birnin wanda ya shahara haikan a sakamakon yawan malumai da kuma almajiran ya kunsa, ya yi kacibus da Mangoliyawa wadanda suka addabi al’umar wannan yankin, a farkon shekarar alif, da dari biyu. Jama’a wannan garin, wadanda suka san irin halin da Mangoliyawa ke da shi, na cin zali da kuma kashe mutane bila adadin, suka yanke shawarar yin hijira inda suka doshi yammacin kasar. A tsakiyar ayarin  wadannan mutanen, akwai wani mutum mai suna  Bahayeddin walad, wanda aka masa lakabi da sarkin mu’addibai. Wannan malamin wanda ya nufi zuwa yankin Konya na kasar Turkiyya, tare da wani dansa, za su zama wadansu shahararrun mutane na wannan yankin. Matashin wanda ya biyo gyatuminsa, shi ne a gaba zai zama mashahurin malamin Sufi nan, wanda aka fi sani da suna Maulana Jaluldden Rumi.

Duk da kuruciyar da yake da ita, a lokacin da mahifinsa ya kwanta dama, sai malamun  wannan yankin suka zabi maulana da ya zama jagoransu. Kuma sun yi haka ne, domin a ganinsu duk jagora nagari, kamata ya yi, a ce ya zama sadikin malami mai hazaka a fannin ilmin addinin Musulumci. Amma kuma shi maulana ya wuce duk yadda suke tsammani, domin bayan tanadar wadannan ababe biyu da suka ayyana, ya tara kyawawan halaye marasa misaltuwa. Maulana wanda aka dinka bada labarin rayuwarsa  a tsawon daruruwan shekaru, ya kasance daya daga cikin manyan misalai na yankin Anatoliya. Malamin wanda yake kiran jama’a da su dinka nazari kan ainahin manufar rayuwarsu a doron duniya tare neman sanin dangantakar da ke tsakanin Ubangiji, mutum da kuma duniya, ya samu karbuwa sosai a kasashen gabas da kuma yammacin duniya. A yankin  Anatoliya inda ya yi ban kwana da duniya kuma, maulana ya samu nasarar shuka kaunar ubangiji a cikin zukatan al’uma. Rubuce-rubuce da kuma kalaman da malamin ya firta sun kasance a sassan daban-daban na rayuwar al’umar wannan yankin, kama daga wakoki zuwa harakar kida. Abinda yasa kawo yanzu ake cigaba da ambaton sunansa a ko ina, tare da kasancewa maburucin da aka fi karanta littafansa a duniya. Badan komai ba mutane ke kaunarsa sosai, face  irin nagarin halin da yake da shi, na taran kowa da hannu biyu, ba tare ya nuna banbancin addinni, launin fata ko kuma kabila ba.

An rawaito cewa a kasar Amirka ma, bayan karatun littafin Injila, litattafan wakokin maulana ne aka fi karantawa. Domin kalamansa  na taba zukatan jama’a. A bisa harshensa ko ababen da ke da wuyar fada na fitowa a cikin sauki. A yayin da a zamaninsa, ba a san komai ba sai tsana da kuma kiyayya, maulana ya samu sa’ar shuka soyayya a tsakanin jama’a ta hanyar amfani da dadadan kalamai masu narke zuciya komai taurinta..

Maulana ya fassara rayuwarsa da kalmomi guda  uku :  ‘’ yin hannun riga da ababen da zuciya ke so, neman magance jahilcinsa, kusantar ubangijinsa ‘’. Duk mutumin da Allah ya halitta ya tanadi wadansu tsarkakkun halaye. Shi yasa, ya dace a ce, ya nemi sanin wadannan halayen. İdan mutum na son yin rayuwar da ta sha bambam da ta kowa, to nagarta da kuma kwarewarsa na gurbacewa. A cikin ruhi  mutum akwai wani ruhi na daban, kuma ba a neman wannan ruhin a waje , domin kasance a cikin gangar jikinmu.

Da haka ne muka kawo muku karshen wannan shirin, sai mu hadu a mako mai zuwa, da yardar mai duka, daga nan Muryar Turkiyya TRT Hausa.

 Labarai masu alaka