Kundin Musulunci: 13

Assalamu alaikum. Barkanmu da warhaka Adam ABUL-BASHAR ne ke fatan kun wuni lafiya, Ina matukan godewa Allah S.W.A sarkin wanda ya halicci sammai da kassai ya kuma bamu damar  da sake saduwa da ku a cikin shirinmu na KUNDIN MUSULUNCI.

Kundin Musulunci: 13

To madallah, zamu fara wannan shirin ne da sunan Allah mai rahma mai jin kai ga muminai a ranar lahira, bayan haka kuma muna yi muku sallam ta musulunci inda muke cewa Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarkatuhu.

A cikin shirinmu na yau, zamu yi kokarin baku labarin dalilin da yasa aka halicci shaidani addinin Islama rudaninsa da kuma hanyar da mutum zai ya kubuta daga gareshi.

Shaidani wanda asalin sunarsa Iblis, wani hallita ne da Ubangiji yayi daga wuta. Dalilin halittansa shi ne saboda yayi wa Ubangiji bauta. Kafin a Allah ya halicci dan adam, sai shaidani na rayuwa da mala’ku ne. Bayan da farkon mutum wato kakanmu Annabi Adam sai shaitani yayi hassada. Da Allah ya bada umarni da “ayi wa Annabi sujjada!” sai shaidani ya kasance mai girman kai da fahariya inda ya fadi a jarrabawan da Ubangiji ya yi masa. Daga baya sai aka bashi suna da ‘Shaidan’ wato hallitan da ya nisanci Allah, wanda bashi da kirki sai laifi.

A cikin Alkur’ani mai girma an bada labarin Shaidani a matsayin makiyin dan adam, wani halitta wanda a kowanne lokaci yake tura mutane da su aikata mugun ayyuka kuma Allah da kanSa ya ce ya aiko dan adam da shaidani a doron kasa a matsayin makiyan juna. Annabi Muhammd S.A.W ya fada a cikin daya daga cikin hadisansa dake cewa, “kamar yadda jini ke bi cikin jikin dan adam, haka kuma shaidani yake...” inda ya kamanta hakan da cewa dangantakar tsakanin dan adam da  shaidani. Kamar yadda jini ke ko’ina a cikin mutum, haka kuma shaidani ke kokarin shiga a ko’inarsa. Ta haka ne yake kokarin fitar da mutum daga shiriya. Shi ya sa idan muka duba haka, zamu gane cewa kamata ne a kowanne lokaci dan adam yayi kokari kaucewa rudani shaidani.

Bayan shaidani ya fadi daga jarrabawan da aka yi masa, sai ya yi alkawarin cewa sai ya nisantar da mutane daga Ubangijinsu domin suka kasance tare dashi a wutan Jahannama, a ranar kiyama. Shi ya idan muka duba a yin Suratul A’râf (aya ta 16-17) Ubangiji na cewa, “Ya ce: ‘To, inâ rantsuwa da halakarwa da Ka yi mini, lalle ne, inâ zaune musu tafarkinKa madaidaici. Sa’an nan kuma hakika, ina je musu daga gaba garesu, kuma daga bâya garesu, kuma daga barin jihohin damansu da barin jihohin hagunsu: kuma bâ zâ Ka samu mafi yawansu masu godiya ba.” Ma’aiki tsitra da amincin Allah su tabbata a gareshi kuma ya ce, a lokacin da musulmi ya yanke shawarar yin aikin kirki, sai shaidani yayi kokarin sa mishi uzuri daban-daban a cikin zuciyarsa, sai ka ga yana kokari ya ga dan adam bai aikata aikin kirkin ba. Idan muka duba wadannan ayoyi da hadisi, zamu ga cewa babban manufar shaidan shi ne ya dan adam ya nisanci Ubangijinsa.

Idan muka duba ayoyin da ke bada labarin jarrabtan shaitani da Annabi Adam da matansa, zamu gane cewa shaidani na duban inda mutum ya yi rauni ne sai ya ja hankalinsa zuwa wurin. A cikin aikin shaidani, wani lokaci yakan fesa karya a cikin kunnuwar mutane; wani lokaci kuma yakan shiga cikin ran mutum, arzikinsa, iyalensa da kuma abubuwan da yake tunanen mutum zai rasa; wasu lokuta kuma yakan yaudari mutum da cewa ya saba da Allah. Shaidani bashi da karfi ko iko akan dan adam. Amma sai dai a kowanne lokaci yana duban idan mutum yayi rauni ne domin ya sa shi ya aikata laifuka.

A cikin addinin muslunci, an siffatan shaidani da dukkan irin mugun aiki. Dukkan mugu da mummunar ayyuka yayi kama da shaidani inda dukkan abubuwa masu kyau suke kama da Mala’iku. A cikin Alkur’ani mai girma, akwai ayoyi da dama dake magana akan haramu, nisantar aikin kirki kamar aiki ne na shaidani. Shi ya sa a lokacin da mutum ke aikata mugun aiki sai ka ji an ce yana aikata aikin shaidani. A cikin rayuwa musulmi, kamata ne a ce yana yaki da shaidani.

Babban alaman shaidani shi ne girman kai. Suratul A’raf (aya ta 12-13) Ya ce: “Mêne ne ya hana ka, ba ka yi sujada ba, a lokacin da Na umarce ka? Ya ce: “Ni ne mafifici daga gare shi, Kâ halitta shi daga lâka. Ya ce: “To, ka sauka daga gare ta: dômin bâ ya kasancêwa a gare ka ga ka yi girman kai a cikinta. Lalle ne kanâ daga masu kaskanci.” A cikin Alkur’ani idan ana bada labarin shaidani yawanci ana magana game da girman kansa ne.

Bayan haka kuma, an gargadi mutane da su nisanceshi shaidani domin wani halitta ne da ke rudin mutane. Shi ya sa rudin mutane, na daya daga cikin alamomin shaidani. A takaice dai zamu iya cewa dukkan siffofin shaidani baya kama da musulmai. Shi ya sa kamata ne musulmi ya bai da hankali kan wadannan abubuwa.

Daya daga cikin alamomin shaidani kuma shi ne sa waswasi a cikin zuciyar mutum. A kowanne lokaci yakan shiga cikin kwakwalwar mutum domin ya bar mutum ya aikata wani laifi. Ya kan bar mutum ya aikata dukkan mugun aiki da sunan cewa aikin kirki ne. Musamanma a lokacin da musulmi ke ibada, zaka sameshi yana damunsa. Yakan nisantar da mutum da ga bautan Allah, yana kokarin nisantar da mutum daga hakkin da ya kamata ya ba Ubangijinsa. Yana sa masa waswasi a cikin alwalansa da sallarsa. Wasu lokuta abinda mutum ba zai yi tunanensa ba, yakan bar mutum yayi tunanensa a lokacin da yake ibada. Shi ya sa yana bar mutum ya kasa samun walwala a cikin ibadunsa.

Shi ya sa, ba bar musulmai da shaidani kadai ba, domin an ba musulmai mala’iku a matsayin abokanni. An bukaci dukkan musulmi da ya dogara da Allah domin ya kubuta daga sharrin shaidani. Allah ya yi wa dukkan mutanen da ke ambatonsa alkawari da cewa zai kiyayeshi. Saboda idan muka duba a cikin suratul (ayata 1-6) Ubangiji ya ce; “Ka ce: “Ina neman tsari ga Ubangijin mutane. Mamallakin mutane. Abin bautar mutane. Daga sharrin mai sanya wasuwasi, mai boyewa. Wanda ke sanya wasuwasi a kirazan mutane. Daga aljannu da mutane.”

To masu sauraro, anan zamu dasa aya, sai mu hadu a mako mai zuwa domin jin wani sabon shirin KUNDIN MUSULUNCI. Kafin nan, ina rokon Allah ya kiyayemu daga sharrin shaidani, Ya shiryar damu Allah madaidaiciya Yasa mu cika da imani... Ameen

Wasallamu alaikum WarahmatullahLabarai masu alaka