Sabbin Manufofin Turkiyya: 13

Barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa damu don jin shirin SABBIN MANUFOFIN TURKIYYA DAGA NAN TRT HAUSA.

Sabbin Manufofin Turkiyya: 13

A shirinmu na yau zamu tattauna lamarin tsarin siyasar Kasashen Yamma wato musamman Nahiyar Turai da kuma Amurka. Kamar yadda wani shahararren malami Ortage Y. Gasset ya rubuta a cikin littafinsa ‘’The Dehumanization of Art’’  ya  bada bayanai game da cewa me yasa mutane suka sha bamban gurin ra’ayoyi ? Ya bada wani tarihin  wani attajiri da ke jinya ya saura kadan ya kwanta dama, sai a gefen katifarsa kuma ga matarsa, sai ga kuma likitoci biyu amma babu wanda ya san me zasu fadi game da wannan mutun,sai kuma wasu matasa biyu na zaune a gurin, A wani gefe guda kuma ga wani dan jarida ya na gaf da rubuta labari sai kuma wani  a zane. Wato, wannan mata ta attajirin, dan jarida da likitocin dukkaninsu shahidun gani da ido ne a lokacin,amma inda an ba kowa damar ya fassara abinda ya gani game da wannan almara da za a sha bamban domin kowa da tunanensa.

Wato abinda muke nufi a nan shi ne, tunanen bil-adama ke janyo banbancin fahimta.  Dalilin haka ne muka ce,abu iri daya na iya faruwa amma idan aka tambayi shahidun gani da ido su bayyana yadda abun ya faru, ba zasu iya bada rahoto daidai ba. Haka zalika a gurin ne ake tattauna wani rahoto ne na hakika wat na gaske. Da haka ake gwagwarmayar akidoji da samun jawabi wadda ya kamata.

Ba wai muna zabar wani rahoto ne mu bar wasu a gefe ba. Muna neman bincike ne na musamman kafin mu amince da wasu bayanai.Gaskiya na nan a bayyane kodayaushe, matukar abin ya zama na gaske, to lalle kowa zai fadi.

Abinda ya kamata mu yi a nan shi ne; mu kebe tunanen mutane masu kama da juna a guri daya sai mu saka alama,sai mu bayyana zantuttuka da suka daidaitu a cikinsu.

Tabbas kowa nada nashi fahimta amma fadin gaskiya abu ne da bai kamata a boye ba. Kowa nada nashi akida da yarda wanda ke rinjayen komai da yake kalla a duniya. A nan ne wasu ke bayar da ra’ayinsu maimakon su bayar da abinda kenan na zahiri.

A yau shuagabannin kasashen nahiyar Turai sun dora ra’ayinsu ga duniya baki daya. Sun shirya dokoki, da kaidojin demokradiya yadda suke so kuma suka bar kowa ya amşnce da hakan. Amma abun ban takaici shi ne, ba kodayaushe ne ake samun gaskiya cikin wadannan akidojin ba.

Maudu’in na yau na kunshi da rikice rikicen dake aafkuwa a nahiyar Turai. Alal misali hari da aka kai a kasar Beljiyom bu ne da ya kamata mu tattauna. Ta’addanci bai da addini, kasa ko kuma akida. Tabbas haka ne. Rikici ko kuma bala’i basu da alaka da al’umma   har abada. Hari da aka kai a Brussel ya yi ajalin mutane wadanda ba su ci baa, ba su sha ba. To shin wani irin addini ne ya ke kirari a yi kisa? To shin akwai wata kabila daake ke kisan wasu kabilu don gyara nata?

Ta’addanci ya zama tsage cikin jiki a duniya a yau. Gwagwarmaya da ta’addanci nada hanyonyi biyu: na farko hadin gwiwar kasa da kasa. Na biyu: sa’annan a yakesu.Tabbas yaki da ta’addanci abu ne mai wuya amma tilas ne a kan kasashen duniya. Babu inda Al’adu ko kuma  zamantakewar al’umma suka nuna kisan kiyashi. A duniya a yau, kasashen Yamma ne suka dandana zafin ta’addanci matuka.

A yanzu dai sai mu ce gwamnatocin kasashen nahiyar Turai sun ga sakamakon tilastawa al’umma akidarsu.

Mu duka mun yi Allah wadai da ta’addanci dake gudana a duniya. Duniyarmu a yau ta zama wani kauye ne. Harin da aka kai a Ankara irinshi ne aka kai a Brussel.  Allah ya tsinewa ta’addanci.

Mun dasa aya a nan. A huta lafiya

        Labarai masu alaka