Sabbin Manufofin Turkiyya: 14

Barkanmu warhaka da kuma sake saduwa damu don jin shirin SABBIN MANUFOFIN TURKIYYA. Zamu tattauna yanayin siyasa a Turkiyya da kuma gwagwarmaya da rikicin kabilanci ashirinmu na yau.

Sabbin Manufofin Turkiyya: 14

Har ila yau wasu suna tada zaune tsaye a kasar ta Turkiyya duk da kokari da gwamnati ke yi gurin magance matsalolin. Idan mutun ya je garin sirt sai ga mutane har da tsofaffi na rike da wuta a hannu don nuna adawanci ga gwamnati. Wasu kuma na janyo fargaba da hawaye a gurare da dama.

Yara kanana na mutuwa,sanadiyar laifi da adawar wasu. Yara basu ci ba basu sha ba amma sune ajalinsu ke yi sakamakon rashin amincewa da juna.Kamata ne ka gana da ni idan na yi maka laifi, kar ka je ga azabtar da yara. Wato har yanzu babu amincewa da juna a Turkiyya.

Har ila yau ana ta hayaniya da juna. Ana ci gaba da zubar da jini, da kuma harbe harbe. Akidar yarjejeniya ko kuma yadda ake gano amincewa da juna abu ne mai muhimmanci. Kamar dai fim ne da aka shirya. A Turkiyya dai an samu hayaniya da kuma gardama tsakanin al’ummar kasar shekara da shekaru. Inda ma aka yi kisan yara sanadiyar hakan. Abubuwa sun rugurguje. An shiga halin kaka ni ka yi, an kasa barci. Ana farkawa daga barci domin tsoro da fargaba. Wato a kowace shekara a bikin Nevruz muna shan shagali da nishadi domin ba wai saboda kakar bazara ba. Amma saboda soyayya da kaunar juna.

AK Parti da sauran jama’a sun fara dakatar da halartar bikin saboda wasu mummunar nufi da wasu keda shi game da sallar Nevruz. Ta yi kokarin kafa manufofi da dama, ta fara aikace aikacen dabarun yaki da ta’addanci. Ta yi tanadin kawo karshen kungiyoyin ta’addanci a birane 11 da suka hada da 

Dağlıca, Aktütün, Reşadiye, Silvan, Urfa, Ceylanpınar har da ma sauransu.Amma har ila yau ana ci gaba da nuna ta’addanci a kasar.

To masu sauraro, ku bar mu tattauna zantuttuka da Farfesa Dakta  Mazhar Bağlı na jami’ar Yildirim Beyazit ya yi game da haka.

Al’ummar kasa sau dayawa suna kan son a samu sakiya.Suna da fahimtar hakan. Tun abunda ya dauki, ruwan sama, kasa ko kuma iska uka na bukatar kirkiran dabaru wanda zai tafiyar da hakan. Dalilin haka ne yasa aka fara gwaje-gwajen  gano yadda za a tafiyar da dabarun.  An ce ana kaunar ita Nevruz domin biki ne na nuna hoduwar kakar bazara. Ana samun iska mai dadi,da kuma ya’yan marmari daban daban.

Gwamnatin Turkiyya ta fara gwagwarmayar tattaunawa da wasu kungiyoyin don magance matsalolin. Ta sake yin hakan ne don sauraronsu watakila sun gano wasu abubuwa da bai dace ba gurin gwagwarmayar magance matsalolin da gwamnati ta fara tun a da’. An yi hakan ne don kawo karshen zubar da jini da ake yi a wasu gurare a kasar. Bayan wasu lokuta ne aka gano sakiya cikin yanayin ‘yan PKK. Wato sun sake dabarunsu, sun ki a maganec matsalolin. Shuagbanninsu ne suka kulla wannan shari da cewa sai dai su ne zasu kawo karshen hakan da son ra’ayinsu. Wani ya isa kadan ya nuna musu iko. A lokacin ne shugaban ‘yan kungiyar adawar ya rinka ihun bana bukatar yancin, bana kaunar koma daga gareku, ina son in kafa wa al’umma mabiyanna guri nan gaba. Ya rinka daga muryarsa a kan batun da cewa sai dai a zubar da jini yau da kullum inda ma Majalisar Dokokin kasar ta yi masa kira. Wannan abu ne kamar dai wasan kwaikwayo a fage.Har yanzu dai sai mu ce basu san ainihin abunda suke bukata ba. Im ba don haka ta yaya za a ce hudowar bazara ne lokacin da wasu zasu rinka kisan mutane. Suna zubar da jini. Suna son su koma da kasar baya kamar dai lokacin da ba a ganin ido da juna. Har ma wasu Kurdawa sun kasa gano fahimta da  yanayin wasunsu. Sakamakon tada zaune tsaye da suke y’ a kasar ne tsar’n demokrad’yar ya karkata.

Wato gwamnati na kokarta hana bambanci da rikici ne tsakanin Turkawa da Kurdawa. Kowa ya san cewa jama’a da dama na son a ce a fitar da Kuradawa a kasar. Wasu sun yadda a tattauana shawarwari ne tsakanin PKK da kuma jam’iyar HDP don a shawo kan matsalolin.Ama san da aka gano filla-filla cewa basu da kaunar hakan.  Dalilin haka ne Turkawa suka ce ba zasu amince su zauna bisa teburun sulhu da Kurdawa ba har abada. Don haka ne da kaina na ce, ga ra’ayi na ba za a samu dace ba. Ba zan iya cewa akwai nasara nan gaba ba domin babu alamar haka.  Akwai wuya matukar wuya da rinjayar Demirtaş dan takara HDP, ko kuma Ocalan shugaban kungiyar PKK da kuma Karayılan wajen sulhu da al’ummar Turkiyya.Labarai masu alaka