Shahararrun Magabatan Turkiyya: 13

Barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa damu don jin shirin SHAHARARRUN MAGABATAN TURKIYYA DAGA NAN TRT HAUSA.

Shahararrun Magabatan Turkiyya: 13

A yau zamu bada tarihin wani malami wadda ina tsamammani kowa ya taba jin sunansa ko daya sau daya ne. Sunansa a asali Muhammad.Ya yi rayuwa a zamanin daular Selcuk. A kasar Iran wadda ake kira Horasana a da’ ne ya zauna wato garin Meshed kauyen Tuş a shekarar alif da hamsin da takwas. A gurin ne aka bashi lakabi Gazzali. Yana daga cikin shahararrun Magabatan Turkiyya. Dole ba za a manta da shi ba har abada.

Zamu tattuana bayanai da Doç. Dr. Güray Kırpık na jami’ar Gazi ya yi game da shi malaminmu Gazzali.

Muhammet ko kuma Gazalli ya bar inda aka haifesa sai ya fara tafiya zuwa gurare don neman ilimi. Da farko ya je Cürcan sai ya karasa zuwa   Nişabur. Ya zauna a matsayin dalibi a Makaranatar  Nişabur Nizamiye Medresesi a wani karancin lokuta sai ya zama mataimakin Limam Cüveynî’. Sai bayan mutuwar shi Cuveyni aka aika  zuwa Bagdad a kasar Iraki a matsayin shugaban makarantar Nizamiye.   Shekarar alif da tisin da daya zuwa  tisin da biyar  ne ya fara koyar da dalibai da kansa. Inda ya rinka tunatar da yadda dalibanci ya ke, yadda malami yake, yadda kuma ake zama da yan ‘uwaye da son juna. Ya rubuta littafi dake kunshi da wadannnan tarbiya mai suna Bidayetu’l-Hidaye inda ya rubuta wasu bayanai game da yanayşn malami: ya ce:

1-Kowane irin halin kunci  mutun ya samu kansa a ciki ya rinka hakuri

2- Malami ya rinka kwantad da hankalinsa

3-  A daina girman kai.

4-Malami ya nemi mutuncin kansa

5- Mai karantarwa ya kaskantar da kansa.Ya yi ladabi

6- Kodayaushe mutun ya rinka tunanen nagarta da alheri.

7- Malami ya zama mutun mara azabtar da yara. Ya zama mai tausayi

8- Kar ya zama malami mai dukan yara ko kuma mai son gaggawa cikin        harkokinsa.

9- Malami ya samu hakuri ya koyar da dalibai wadanda kansu bai da gaggawa daukar abubuwa. Kar ya yi hushi da dalibai idan sun kasa gano abunda ake bukata.

 10- “Kar malami ya yi kunyan cewa bai san wani abu ba.

11- Ya zama mai gyara hanyar dalibai

12-Ya kokarta gano amsoshi da dalibai zasu yi masa.

13- Ya amince da shahidu

14- Ya  sake gyara kuskure da dalibi ya yi

15-Malami ya kokarta tsare dalibai kamar dai mahaifinsu.

16- Malami ya nemi yardan Allah

17- Ya samu dabarun kara masu karfi da kwazo

Imam Gazzal, ya yiwa dalibai nasiya da cewa:

1-Dalibi ya rinka ya isar da sallama idan ya gamu da mutane.

2-Kuma  dalibi ya zauna kurun. Kar ya zama mutun mai sababbi.Ya rinka bin dokokin malaminsa.

3- Dalibi ya nemi izin kafin ya amsa ko kuma ya yi tambaya. Kar yay i aiki da son ransa.

4-Kar dalibi ya nunawa duniya cewa ya fi malaminsa sanin abu.

5-Ya yi hira da abokansa amma bag a malaminsa ba.

6- Ya zauna ya nasu kar ya yi juye juye gurin koyon karatu.

7-Dalibi ya maida hankali gurin koyon karatu.

 8-Ya yi ladabi ya zauna har sai malaminsa ya ce an kamala.

9-Kar ya gajiyar da malaminsa

10- Kar ya rinka tambaya a kan hanya idan ya ga malaminsa na tafiya.

11-Kar ya yi kuskure malaminsa ya gansa da aikata mummauan aiki. Domin abun zai kawo matsala nan gaba.

Imam Gazzali ya yi nasiha ga malamai, dalibai, iyayen yara da sauransu. Ya ce:

1-Bai kamata malami ya zama mutun mai hushi kodayaushe ba.

2-Ya zama malami mai tausayi da yin tuba ga ubangiji rayuwarsa ya zama abin kwaikwayo ga dukkanin jama’a.

3-Yara dalibai da yake koyarwa su dauki aikin nagarta da yake yi.

4-Kar ya zama malami me kai kawo yana sake gurin zama.

 5- Kar ya zama mutun da za a saya da dukkiya ko kudi.Hak kuma kar sarakai ko kuma aattajirai sun rinka nuna ifonsu ga malami.

Ga ra’ayin Imam Gazzali,idan dalibai suka tsinci malaminsu cikin halin kaka ni ka yi, su taimaka. Zancen karshen shi ne, kar dalibi ya rinka zuwa gurin malamai yana caanzasu . ba dabi’ar kirki ba ne. Dalibai su zama masu bin dokokin da aka kafa tun ranar da suka shiga makaranta.Labarai masu alaka