Shahararrun Magabatan Turkiyya: 14

Barkanmu da warhaka da kuma sake saduwa damu don jin shirin SHAHARARRUN MAGABATAN TURKIYYA daga nan TRT Hausa.

Shahararrun Magabatan Turkiyya: 14

A yau zamu bada tarihin wani jarumin Turkiyya mai suna Ahi Evran. Masani, mai nazarin tattalin arziki da kuma suffi. An haifesa a Hoy a kasar Azabaijan a shekarar alif dari da sabain da biyu inda ya  koma ga ubangiji a shekarar alif dari biyu da sittin da daya. Sunansa a asali Nasirudeen Ebul Hakayik Mahmud Bin Ahmet. Ya fara karatunsa a garin Hoy sai ya ci gaba a Horasana  a gurin babban malami Faahreddin Razi inda kuma ya koyi karatun Al qurani da falsafa. Ahi Evrân ya  zauna gurin Hoca Ahmet Yesevi’ a matsayin dalibi lokacin da yake matashi. Ya koyi karatun tasawwuf sosai.

Ahi Evran, ya kafa cibiyar raya akidar aikin nagarta, sana’a girmama baki da son juna inda ya kafa cibiyar Ahilik. Ita Kungiyar ta zauna shekara da shekaru tana koyar da jama’a yadda ake kokarta son juna da zamantakewar al’umma.  Ahi Evran, da matarsa  Fatıma Bacı ne suka yada al’adun ahilik a duniya domin yayinda yake gwagwarmayar yada wanna al’ada ita matarsa kuma ta kafa kungiyar mata ta ahilik wanda ake kira Baciyan Rum a yankin Anatoliya wadaa ya haifar da wasu kungiyoyin mata a yankin.   Ahi Evran,da kansa yana da sana’o’i sama da talatin inda ya koyar da matasa da dama. Wato ya kafa Ahilik ne da nufin gudanar da harkokin nagarta, tunanen kirki, kimiyya da kuma aiki.

Ahi Evran, ya taho da malamansa  Evhadüddin Kirmani  da kuma  Muhyiddin Arabi ne a yankin Anatoliya a shekarar alif dari biyu da biyar 1205 inda suka yi zagaye a yankin. A gurin ne suka fara farkar da jama’a muhimmancin rayuwa mai kyau nan duniya da kuma lahira. Sun rinka bawa jama’a nasiha mai kyau. A gefe guda kuma ‘yan Mongoliya suka farwa guraren da yaki. Ahi Evran da yan uwayensa sun kokarta fafatawa da su ‘yan Mongoliya.

Bayan ya taho yankin Anatoliya ne shi malaminmu Ahi Evran ya je garin Kayseri da zama inda ya kafa zauren sana’ar fata ya rinka sakar abubuwa da dama da fata. Aiki dake faranta masa rai. Kungiyar Ahilik din da ya kafa ya shahara a lokacin a koina. Sakamakon haka ne ya zama gwarzo furin sana’o i sama da talatin  da ilmantar da matasa a duniya a tarihince.

A shekarar alif dari biyu da ashirin da bakwai 1227 ne ya je birnin Konya lokacin da sarkin daular Selçuk Sultanı Alaaddin Keykubad ke kan mulki. Ya yi aiki a matsayin mai karantarwa a gurin, aya yi nunin abubuwa da ya samar wa sarkin daular. Bayan kisan Alaatin Keykubat da aka yi ne ya tsere zuwa Kirşehir da zama.

Ya zauna garin Kırşehir shekaru biyar kuma a lokacin ne yan Mongoliya suka kwace ikon wasu yankunan Turkmen suka ta nuna musu azaba da barazana. A nan ne aka nada Nureddin Caca bey a matsayin magajin garin Kirşehir. Sai ya samu damar zirga zirgar raya al’adun Ahilik musamman a tsakiyar Anatoliya.  Da haka ne abun ya shara a  Ankara, Aksaray, Çankırı, Kastamonu da sauransu. A nan ne sarki Nureddin Caca ya dauki matakin karawa da ‘yan Mongoliya. Yan Mongoliya dai sun yi ksisa da dama a yankin a lokacin. Dai dai lokacin kuma akwai dan Mawlana Rumi mai suna Alaaddin Çelebi.

A shekarar alif dari biyu da sittin da daya 1261 ne Allah ya yi masa rasuwa. Amma san da aka rinka tunawa da shi kodayaushe domin himma da ya nuna  fannonin sana’a da kuma aikin nagarta. Daya daga cikin litattafansa ne  “fütüvvetname”  wadda ya syadu a fadin duniya baki daya. A daular Uthmaniya ma an ci gaba da gudanar da al’adun Ahilik bayan mutuwarsa.

A yau mutun zai ga kabarin shi malaminmu  Ahi Evrân’ a garin Kirşehir unguwa da ake kira Ahi Evran Mahallesi a cikin masallacinsa ne akwai kabarinsa.

A nan muka kawo karshen shirinmu na yau da fatan zamu yi kwaikwayo da mazan kwarai shahararrun magabatan Turkiyya. Ma’asalaam.Labarai masu alaka