Kokarin Turkiyya na samar da tsaro a Gabas ta Tsakiya

Tun daga lokacin da aka fara hare-haren tsaron Fırat, wasu ba su san sunar yankin Al-Bab ba amma a halin yanzu Turkiyya baki daya da wasu kasashen yankin Gabas ta Tsakiya na maganar game da yankin.

Kokarin Turkiyya na samar da tsaro a Gabas ta Tsakiya

        Masoya gidan rediyon muryar Turkiyya wannan shi ne dalilin da ya sa a cikin shirirnmu na wannan mako muka ce bari mu tattauna game da hare-haren Tsaron Fırat da kuma al’amurran da ke faruwa a yankin Al-Bab.

        Türkiye Cumhuriyeti uzunca bir süredir DEAŞ, PKK ve FETÖ başta olmak üzere onlarca terör örgütüne karşı ciddi bir mücadele veriyor. Tüm engellemelere rağmen Fırat Kalkanı Operasyonu da başarıyla sürüyor. Jamhuriyar Turkiyya ta dauki tsawon lokaci tana yaki da kungiyar ta’adda ta Daesh, PKK da kuma PKK. Ko da yake suna da matsaloli amma kasar ta yi nasara wurin kai hare-haren tsaron Fırat.

        A cikin tsaron Fırat da aka yi, tsawon kwanaki 10 da suka yi da tsakanin Çobanbey-Cerablus; dakarun Free-Syrian Army sun yi nasarar korar kungiyar ta’adda ta Daesh  a Dabık karkashin jagorancin jami’an tsaron Turkiyya inda suka koma a Al-Bab. Amma sai dai shiga Al-Bab ba karamin aiki bane. Mutanen da ke Al-Bab na yankin arewacin Aleppo, sun fi muutanen da ke Çobanbey, Dabık ve Cerablus. Ko da yake Jami’an tsaron Turkiyya tare da dakarun Free-Syrian Army sun yi nasara a kudancin Al-Bab amma sai dai basu iya sun nasarar garin baki daya ba. A halin yanzu jami’an tsaron Turkiyya, Dakarun Free-Syrian Army da kuma dakarun Türkmen (dakarun da ke karkashin jagorancin Muntasır Billah Tugayı, Fatih Sultan Mehmet Tugayı da  Sultan Murat Tümeni).

        Kamar yadda muka fada muku a cikin shirinmu na makonmu da ta gabata, saboda tsanyi jami’an tsaro na kai hare-hare a hankali ta yadda ba zai taba fararen hular yankin ba. Bayan haka kuma kungiyoyin Daesh da PKK/YPG na cikin matsaloli. Da yake kawancen kasashen duniya da sojin gwamnatin Assad na yaki a yankin da Daesh ta ke shi ya sa ne Daesh ta rasa abin da zata yi sai dai ta koma zuwa Al-Bab. Kawancen kasashen duniya karkashin jagorancin Amurka kuma ta saya a Mosul. Ta haka ne Al-Bab ya zama wuri daya tak da ake yaki da Daesh kuma wannan wuri kasar Turkiyya kaida ce ta ke yaki da ita. Wato wannan shi ne dalilin da ya kamata ‘yan siyasa da ‘yan jaridu da suke yiwa Turkiyya sharri akan cewa tana taimakawa Daesh, ta ba hakuri domin karya. A yankin Al-Bab, ana tunanen akwai masu kai harin kunar bakin wake kusan 300. Bayan haka kuma kungiyar na tilasta fararen hula da suka harin da basu shirya ba.

        Ko da yake ana cikin mawuyacin hali amma sai dai jami’an tsaron kasar Turkiyya da dakarun Free-Syrian Army na tsayin daka wurin yaki da kungiyar. Idan dakarun Free-Syrian Army karkashin jagorancin jami’an tsaron Turkiyya suka kori Daesh a Al-Bab, to babu shakka kungiyar ta’addan zata shiga cikin matsala babba a Siriya. Hakan kuma zai zama sanadiyyar kawo karshen kungiyar ta’adda PKK/YPG da ke yankin. Bayan an yi nasarar kwace Al-Bab, to jami’an tsaron Turkiyya da na Free-Syrian Army zasu koma zuwa Münbiç, Rakka da Afrin. Bayan haka kuma sai a fara tunanen yadda za a warware matsalolin Aleppo.

        Bayan an karbi Al-Bab, akwai al’amurra biyu da zai iya faruwa. Ko jami’an tsaron Turkiyya da dakarun Free-Syrian Army zasu yaki kungiyar PKK/YPG a Munbiç da Afrin wanda babu shakka zasu yi nasara ko kuma za a dakatar da tashin hankali sai a tattauna ta Siyasa. Idan ya dace cewa za a daya cikin biyun, wato inda maganar Munbiç da Afrin to Turkiyya da Amurka ne zasu shugabanci wannan al’amari. Saboda a Munbiç akwai sojin Amurka. A gefe guda kungiyar PKK/YPG da dakarun demokradiyyar Siriya da ke yaki da Daesh a Munbiç suna samun taimakon kungiyar ta’adda ta Daesh ne. Anan fa’ida da Turkiyya ta ke da shi a Münbiç shi ne; a baya akwai alkawarin da Amurka ta yiwa Turkiyya. Ta wannan hanya ne Amurka ba zata kiyaye kungiyar PKK/YPG ba.  Tabbas, idan ranar ta kai  zamu duba in Amurka zata cika alkawarinta.

        A halin yanzu Rakka ya sa Turkiyya da Amurka sun kusanci juna akan yaki da ta’addanci da ake yi a Siriya. Ko da yake Amurka na cewa kungiyar PKK/YPG ba kungiyar ta’adda ba ce shi ya sa ke suka taimaka musu. Kuma an bude wani sansani a yammancin Rakka. Dalilin da ya sa suka yi wannan abu shi ne suna son su kewaye Rakka tare hana Turkiyya hare-haren Tsaron Fırat da take yi. Ta haka ne Amurka ta bukaci ita da Turkiyya su yi aikin hadin gwiwa.

        A cikin yarjejeniyar da Turkiyya, Iran da kuma Rasha suka sanya a cikin a ciki, basu kara kungiyar PKK/YPG a cikin mutanen Siriya da za a wasu abubuwa akamar “yanci”, “demokradiyya” da sauransu. Amma sai dai abin ciki ne a lokacin da Turkiyya ke yaki da ta’addanci a Siriya, kasar da taimakamata ita ce kasar Rasha. A yayin da Turkiyya da Rasha ke hadin kai ta hanyar diflomasiyya, a gefe guda kuma Amurka da Tarayyar Turai sun ja baya. A cikin wata bayanin da Rasha ta fitar a ranar 20 ga watan Janairun shekarar 2016, “Turkiyya, Iran da Rasha zasu jagorancin taron zaman lafiyar Siriya, kuma an amince da hakan ne domin a samu sauki wurin yin hakan.” Wannan jumala ne dalilin da ya sa za a gudanar da wannan taro.

        Idan muka duba, ma’anar Al-Bab shi ne kofa. Bayan Al-Bab za a gano cewa wasu kasashe yankin zai budewa kofa, wasu kasashe kuma za su rufe kofar. Tabbas ba zamu iya fadin komai game da matsayin kasar Amurka  yanzu ba, domin kafin mu iya fadin hakan sai mun jira har sai ranar 20 ga watan Janairu a lokacin da Trump ya hau karagar mulki.Labarai masu alaka