Munanan abubuwan da Trump zai gada daga gwamnatin Obama a kasashen waje

Kusan makwanni 2 suka rage Donald Trump ya dane kujerar mülkin kasar Amurka. Wannan lokaci na karatowa kuma hare-hare a kasashen duniya na kara yawaita. Akwai kungiyoyin ta’adda daban-daban masu sunaye daban-daban amma kuma manufarsu guda daya ce.

Munanan abubuwan da Trump zai gada daga gwamnatin Obama a kasashen waje

Kusan makwanni 2 suka rage Donald Trump ya dane kujerar mülkin kasar Amurka. Wannan lokaci na karatowa kuma hare-hare a kasashen duniya na kara yawaita. Akwai kungiyoyin ta’adda daban-daban masu sunaye daban-daban amma kuma manufarsu guda daya ce. Sakamakon haka suke ta kai hare-hare a kasashen duniya da dama da suka hada da Turkiyya.

A daidai lokacinda shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya ke ta kare manufar da a samar da wani yanki na zaman lafiya a kasar Siriya, sai ga shi a kasar Faransa da francoir Hollande ya ke mülki an mayar da kasar kamar kogin zubar da jini. An kashe Faransawa ba adadi a kasar Faransa inda tsawon shekara 1 kenan ana shugabantar kasar da dokar ta baci.

Kuma hakan bai is aba, sai da gwamnatin Faransa a wani bangare na yaki da ta’addanci ta kwace dukkan wani karfi da bangaree shari’a na kasar ya ke da shi.

Haka kuma a daiidai lokacinda shugabar gwamnatn Jamus Angela Merkel ke goyon bayan Erdoğan game da a samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Siriya, ita ma kasarta na fama da matsalolin ta’addanci.

Daga cikin kasashen Yamma kasar Amurka ce kadai tilo da ta fito karara ta nuna rashin amincewa game da matakan samar da zaman lafiya a kasar Siriya wanda shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya nuna da a samar. Kuma wasu kasashen Tarayyar Turai sun yi shiru game da hakan tare da taimaka wa manufofin Obama na zubar da jini. Shugaba Obama da dakarunsa sun sor ikicin kasar Siriya ya ci gaba kuma duniya ta zuba idanu tana kallo. Kuma kasar Iran da ta ke adawa da Amurka ta shiru abun kamar wasa wannan abu.  

Kuma yadda Turkiyya ta zama kasa daya tak da ta ke kare kasar Siriya tare da samar da zaman lafiya a kasar Siriya abu ne da ya ke da jan hankali sosai.

Kuma abun ya yi wahala da tsada yadda ‘yanci, zaman lafiya, kwanciyar hankali da demokradiyya a kasar Siriya.  A ‘yan makwannin da suka gabata kungiyoyin ta’adda da suke da mambobi a Siriya da Turkiyya na PKK/PYD da Daesh na kai hare-hare a Turkiyya kai tsaye inda suke kashe ‘yan sanda, sojoji da sauran jama’ar kasa.

Kasashen Turai da suke cikin kungiya daya da Turkiyya suna zanga-zanga ne tare da la’antar wadannan hare-hare da ake kai wa ta Turkiyya suna mika sakon ta’aziyya. Kuma an kyale Turkiyya ita kaai a yaki da Daesh da ta ke a kasar Siriya. Wannan wani lamari ne mai kama da wasan kwaikwayo.

Kuma Amurka da ta ke kawar Turkiya, Tarayyar Turai da Rundunar tsaro ta NATO sun yale dakarun Turkiyya suna yakida ‘yan ta’adda su kadai a Siriya. Kuma Amurka da sauran kasashe sun kawo kayan yaki na sama zuwa Turkiyya.

Duk da kyale ta kasai da kawayenta suka yi, Turkiyya ta shiga kasar Siriya tare da yakar ‘yan ta’addar Daesh. Kusan shekaru 4 kawancen kasashen duniya karkasin jagorancin Amurka suna kai wa Daesh hari a kasashen Siriya da Iraki amma babu wata nasara guda 1 da suka samu. Amma ga shi Turkiyya da sojojinta 300 da tankoki 15 suna share ‘yan ta’addar Daesh da na PYD a arewacin Siriya. Kuma ana nasarar wannan yaki ba tare da neman taimakon Amurka na hari ta sama ko kuma bayanan sirri ba.

Adaidai lokacinda Turkiyya ke samun nasara kan ‘yan ta’adda sai suke kai hari a manyan biranen kasar. ‘Yan ta’addar Daesh, PKK/PYD na kashe sojoji, ‘yan sanda fararen hula. Sun kashe daruruwan mutane a kasar. Kamar yadda ya ke a kowanne lokaci, kawayen Turkiyya na yammacin duniya na sukar hare-haren ne kawai, wasu lokutan ma wasun su ba ma sa ambatar sunan ‘yan ta’addar PKK/PYD.

Bayan da Daesh ta kai hari a abirnin Istanbul a daren ranar sabuwar shekara kasashen yammacin duniya sun mayar da wani martani mai ban mamaki. Kungiyar NATO da ta ke inuwar kasashen Yamma ta sauko da tutocinta kasa kasa. Asali irin wannan martani ya kamata a dinga mayarwa. Saboda sojojin Turkiyya sojojin NATO ne ai. Amma sai ga shi NATO ba ta sakko kasa da tutocinta saboda kashe sojojin Turkiyya amma saboda an kashe fararen hula sai ga shi sun sakko da tutocin.

Halayyar NATO game da haka a bayyane ta ke. Ana kashe daruruwan sojojinta amma ba ta sakko da tuta, amma saboda an kai hari kan wani guri da ake yin abu daidai da tsarinta sai ga shi sun sakko da ita.

Wannan halayya ta NATO tabbas ta siyasa ce, da kuma nuna rashin tarbiyya. Kungiyar NATO ba ta taba nuna bakin ciki da yin makoki sakamakon kashe daruruwan mutane da PKK da Daesh suka yi ba, amma kuma a harin gidan rawa na daren shiga sabuwar shekara sai ga shi sun yi zaman makoki.Labarai masu alaka