Shin tsarin Majalisar Dinkin Duniya yana aiki a yanzu?

Shin tsarin Majalisar Dinkin Duniya yana aiki a yanzu?

Shin tsarin Majalisar Dinkin Duniya yana aiki a yanzu?

Shekarar 2016 ta zama wata shekara da ta ke cike da abubuwan bakin ciki. Shekarar 2016 shekara ce da aka y ifama da ta’addanci a cikin kasashe da matakin kasa da kasa, rashin daidaiton tattalin arziki, yakn basasa, balahirar ‘yan gudun hijira, rasa rayukan mutane da ba su ji ba su gani ba da kuma matsalar talauci da yunwa a wasu kasashen duniya.

Idan har muna so shekarar 2017 ta zama daban da ta 2016. Dole mu hade kanmu waje guda ba tare da kallon Addini, Al’ada, launin fata koy ankin da muka fit oba, tare da kare martaba da darajar dan adam.

Kuma an san cewa, yanayin kasa da kasa ya munana a yanzu. Tsarin Majalisar Dinkin Duniya ba ya aiki. Duk da bukatar yin sauye-sauye na gaggawa, amma mambobn kwamitin tsaro na Majalisar ba sa so a tattauna wannan batu. Wani bangaren na Majalisar na yi aiyukan da suka kamata. Amma kuma shugabancin majalisar ba ya tabbatar da ame aka cimmma a aikace.

Amurka da Tarayyar Turai da suka hade kai waje guda sun kasa samun nasarar shawo kan rikicin kasar Siriya, yakin basasar Iraki, balahirar ‘yan gudun hijira, ta’addanci a kasashen duniya, kütse a yanar gizo, da wasu matsaloli da dama da ke damun wannan duniya tamu.

A daya gefen kuma, a yau shugabancin Turai ya rasa kansa da manufarsa. A yau ba a daukar wani mataki a nahiyar Turai ko a wan, babban birnin wata kasa ba tare da neman taimakon Amurka ba. A shekaru 8 da suka gabata gwamnatin barack Obama ta munanta yanayin tsaro a duniya da sunan tana aiwatar da manufofin samar da tsaro.

A yanzu kuma za mu ga yadda gwamnatin Donald Trump za ta yi kan irin wadannan abubhuwa a kasashen duniya, shin za ta iya magance su tare da daukar matakan da suka amata.

A gefe guda kuma, ana fuskantar matsalar manufa da shugabanci kuma za a ga yadda zai kusanci batun kasashen Schengen da kuma batun balahirar ‘yan gudun hijira da ma alakar Turkiyya da Tarayyar Turai.

Kungiyoyin ta’adda na PKK, Daesh da FETÖ na Gulen da Tarayyar Turai ba sa kallon irin barazanar tsaro da suke yi wa Turkiyya, a wani bangaren kuma suna cewa, suna kokarin ba wa Turkiya darussan demokradiyya amma kuma suna taimakawa tare da marawa ‘yan ta’adda baya. Suna ba wa wadanan ‘yan ta’adda damar zama a kasashensu.

A shekarar 2017 akwai kasashe da za a gydanar da zabuka wadanda a c,kinsu an samu tsaurarawar matsalolin kyamar Musulunci, wariyar launin fata da kyamar bakin ‘yan kasashen waje. Wadannan zabuka za su bayar da makomar Turai da irin shugabancinta.

Turkiyya a shekarar 2016 na bankwana da hare-haren ‘yan ta’addar PKK da Daesh da kuma yunkurin juyin mülkin da ‘yan ta’addar FETÖ suka yi a ranar 15 ga watan Yuli.

Kasashen Turai da na Rundunar tsaro ta NATO da suke kawayen Turkiyya ba su tsaya tare da kasar ba a halin da ta shiga na fama da ‘yan ta’adda. Sun mata cewa, tsaron Turkiyya ya kasance wani bangare na tsaron kasashen Turai. Misali idan ana maganar yaki da ta’addanci a matakin kasa da kasa, to kasashen Turai ba s aba wa biranen Istanbul, Ankara, Baghdad ko Islamabad taimakon da ya kamata, amma kuma idan a biranen Paris, Brussels ko Nice to hakan matsala ce, kuma babu wata matsala a tsakanin wadannan birane. Wakilan ‘yan ta’addar PKK suna yawo a biranen kasashen Turai tare da tara wa kungiyar kudi, suna samarwa da kansu sabbin mambobi, suna bayyana a kafafan yada labarai tare da yada manufofinsu kai ta kai ga suna zuwa majalisun dokokin kasashen Turai suna yin jawabi kuma ana tafa musu. Kuma hakan na faruwa ne duk da tarayyar Turai ta ce ta amince da kungiyar PKK a matsayin kungiyar ta’adda. Kuma Tarayyar Turai ta rufe idanuwanta tare da kasa kallon abubuwanda PKK suka yi wa Kurdawa a shekaru 10 da suka gabata, inda suka amince cewa, PKK na kare manufar Kurdawa ne.

Kuma wannan PKK na kama da tsarin Neo Nazi ko kuma wasu jama’a da ke neman halarta kansu kan Amurka.

Kai Amurka ba ta bayar da taimako ga hare-haren tsaron Firat da Turkiyya ke kaiwa ‘yan ta’addar Daesh a arewacin Siriya.  A maimakon haka sai gwamnatin Obama ta ke ci gaba da ba wa reshen PKK da ke Siriya makamai wato YPG.

Duk da irin wannan suka, Turkiyya ta yi kokarin kwace jama’ar Aleppo dubu 45 zuwa Idlib.  

Watakila babban abin da ya fi mamaye kafafan yada labarai a karshen shekarar 2016 shi ne, yarjejeniyar tsagaita a dukkanin Siriya da Turkiyya da Rasha suka cimma a ranar 30 ga watan Disamba. A yayin wannan tattauna wa bangarorin adawa da na gwamnatin Siriya sun zauna a teburin Sulhu tare da cimma matsayar tsagaita wuta.

Zaman Astana an shirya shi ne saboda a cike kokarin da aka yi ta yi a Geneva a baya wanda aka kasa cimma matsaya.

Idan aka kalli shekarar  2017, za mu ga cewa akwai manyan matsaloli da aka kasa shawo kansu. Za mu ga yadda manyan kasashen duniya ke rikici da juna, misali a kasar Yukren, Siriya, da kuma kasashen Asiya da na Balkan.

Kasashen duniya sun kuma kasa shawo kan wannan matsala da ake ta fuskanta.

Ganin yadda aka bar dimbin matsaloli a shekarar 2016, to akwai bukatar a hada kai baki daya tare da maganin wadannan matsaloli a dukkan matakai. Wannan wajibi ne a kan kowa da ya bayar da gudunmowa wajen magance matsalar da dan adam ya ke fuskanta.

 Labarai masu alaka